Labarin Malam Mai Makara ya Zagaye Kafafen Sada Zumunta a kan Yanda Yake Ƙona Al'qurani don maganin 'Yanbindiga

top-news

Shin Dagaske Malam Mai Makara Yana Ƙona Al'qurani...?

Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times 

Malam Mai Makara, sunan da Yayi Fice kenan wanda kowa yake kiransa da shi. Ɗan Asalin Maiduguri da ya samu mazaunina Dutsinma (ko da yake ba dindindin yake zaune a garin ba)  Cecekuce ya cika kafafen sada zumunta na zamani akan cewa Malam Mai Makara yana haka Ƙabarai ya sanya Al'quranai a ciki ya ƙona wanda idan yayi hakan zai maganin hare-haren barayin daji masu garkuwa da mutane.

Binciken Katsina Times ya gano cewa Malam mai Makara Malamin Tsibbu ne da yake amfani da salon yaudarar mazauna ƙauyuka da suke fama da firgicin 'yan bindiga yana karbar masu kudade ta hanyar biyo da salon Damfara inda yake wasu abubuwa na kawar da hankali ko tunanin mazauna ƙauyukan.

Malam Mai Makara Yana Ƙona Al'qurani...? 

Malam Mai Makara baya Ƙona Al'quranai, Babban abinda yake aikatawa shine: zai shiga Ƙauyuka ya nemi su hada masa kudade kamar Miliyan daya ƙasa ga haka ko fiye, za a yanka Dabbobi kamar raguna, daidai da karfin kauyen da ya shiga, sana  zai kawo Makara, da Al'quranai a zuba a cikin makarar, a dauka ana zagaya gari da ita, bayan an haƙa kabari an samu tsaffin Kujeri irin na Mata, da wasu kayan surkulle,  an zuba a Ƙabarin sai a kunna Wuta har ta ƙone komai da aka zuba a Ƙabarin. 

Ance Duk garin da yayi wannan Surkulle, babu shi babu shigar 'Yan bindiga, idan ma suka shiga basa iya komai, ko kuma suyi ta Mutuwa.

Wanda Ruwa ya Ci Idan Aka mika masa Kaifin Takobi Kamawa zai Yi.

Da yawa daga Mutanen Ƙauyuka sun yi Imani da abinda yake aikatawa duba da yanda malamin yake samun karɓuwa. Katsina Times ta gano cewa malamin ya shiga Ƙauyukan Batsari, Safana, Danmusa, wasu yankuna na Kankara da Dutsinma, da Jihohin Zamfara da sauransu.

Ance a wasu kauyuka baka isa ka ce, Malam mai Makara ba daidai yake ba, mutanen kauyen zasu taso kanka.

Matasan garin Batsari Basu yadda dashi ba sunyi Nufin kunyatashi duk sanda yace zai aikata haka a cikin garin Batsari duba da yanda Duk garin da yaje yayi wannan Surkulle da wuya a kwashe kwana uku barayi basu shiga garin sunyi Barna ba.

An samu Malaman Tsibbu Iri daban-daban da suke amfani da yanayin halin da al'umma suke ciki na rashin kwanciyar hankali suna shirya salon Damfara don neman kudi a Wajen masu rauninin Tauhidi. An samu malamai da suke karyar Maganin Bindiga a yankunan da ake fama da wadannan tashe-tashen hankullan.

Wakilan Katsina Times sun taba bin Diddiƙin wasu masu bada maganin bindiga a wani kauye dake tsakanin Zamfara da Katsina, inda muka iske kasuwa ta bude, a cikin daji inda 'yan Damfarar suke bada maganin Bindiga, abin mamaki hadda manyan mutane ke zuwa don karba.

Yanda suke bada Maganin Bindigar shine: A cikin Daji Saman Duwatsu, ba a zuwa wajen masu bada maganin da Takalma a kafafun ka, idan kuma ka samu kuskuren zuwa da Takalmi, babu komai wannan sunansa kuskure. Sana ko wane Boka ya raba yaransa masu Tarbo baki, ga alama wanda yafi kawo mutane shi yafi kamasho mai tsoka, shi yasa ma zakaga idan kazo wajen a matsayin Bako zakaga kamar kaje kasuwa Layin 'Yan Fura-fura. (Malam Zo nan, Malam ga wata mai kyau ce) haka za'aita kiranka har ka rasa wajen Bokan da Zakaje.

Wakilin Jaridar Katsina Times dai yaje ganin Ƙwam, bin Diddiƙi da Kwalailaita, ya Amso maganin Bindiga na Sha da na Wanka, amma jiya daƙyar ya sha, a lokacin da Sojojin Nijeriya suka bude wuta ga wani rikici da ya barke a unguwar Chake cikin birnin Katsina tsakanin su da Matasa, wanda yayi Sanadiyar Kashe Yaro da bai gaza shekaru goma ba, da jikkata biyu, kone-kone da harba Tiyagas a cikin Unguwa don kwantar da tarzomar. Abin da ya rage ga 'Yan Damfara Malaman Tsibbu, shine su yo Maganin Tiyagas don masu cutar Asama na fuskantar Barazanar Mutuwa a lokacin da Jami'an tsaro suka harba Tiyagas don kwantar da Tarzoma

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *