GWAMNAN JIHAR KATSINA YA BADA UMURNIN A SOMA SAYAR DA HATSI AKAN NAIRA DUBU ASHIRIN KOWANE BUHU.

top-news


      Gwamnan jihar Katsina, Dakta Dikko Umaru Radda ya bada umurnin a soma sayar da MASARA da GERO da DAWA na Gwamnatin Jiha, ga jama'a akan Naira Dubu Ashirin kowane buhu.

      Gwamna Dikko Radda ya bada umurnin hakan ne a yau Jumu'a, 8/3/2024 jim kadan bayan ya kaddamar da babban Kwamitin rabon hatsi da dafaffen abinci na jiha da kuma na kananan hukumomin 34 na jihar Katsina, a dakin taro na gidan gwamnati.

      Ya yi bayanin cewa gwamnatin jiha ta sayi buhu Dubu Saba'in da Biyu da Dari Biyu na masara da gero da dawa inda za a kai buhu Dari Biyu a kowace Mazaba 361 dake fadin jihar nan.

      Dakta Dikko Umaru Radda ya kara da cewa an kayyade cewa za a iya sayar adadin da buhu daya ne kadai ga gungun Mutum Biyar.

      Gwamnan ya kuma ce gwamnati ta kammala tsarin shirin rarraba dafaffen abinci kyauta ga mabukata tun daga ranar daya ga Watan Ramalan mai kamawa har zuwa karshensa in Allah Ya kai mu.

       A karkashin wannan shiri, Malam Dikko Radda ya ce an yi tanadin rarraba ingantacen abinci domin buda baki ga Mutum Dubu Saba'in da Biyu a kowace rana, a cibiyoyi dandaban da za a bude a ko'ina cikin fadin jihar Katsina.

      Hakan ya nuna cewa ta wannan sabuwar hanyar da aka kirkiro, gwamnatin jihar Katsina za ta ciyar da jama'a mabukata sama da Miliyan Biyu a cikin Watan nan Maialfarma dake tafe.

      Bugu da kari kuma, Gwamna Dikko Umaru Radda ya sanar cewa gwamnatinsa ta tanadi buhun shinkafa mai cin kilo 25, wanda za a raba kyauta ga Mutane Dubu Talatin Da Uku (masu bukata ta musamman da gajiyayyu da tsofaffi marasa sukuni).

       Gwamna Dikko Radda ya yi bayanin cewa gwamnatin jihar Katsina ta dauki wadan nan matakai ne don kokarin karya farashin abinci, wanda ya yi tashin gwabron zabo, da kawo sauki ga al'umma, da kuma ciyar da abinci ga masu rauni a cikin Watan Azumi dake tafe, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

     Don haka, ya yi gargadin cewa dukkan shirye - shiryen an tanade su ne domin talakawa masu bukata, don haka kada a ga wani mai sukuni na kokarin saye, ko shiga layin amsar abinda za rarraba ma masu rauni.

      Saboda haka ya bukaci wakilan Kwamitocin da aka kafa da su sanya ido sosai, su tabbatar an yi adalci a wajen aiwatar da wadan nan aiyuka kamar yadda gwamnati ta tsara don amfanin talaka.

       Ya kuma yi kira ga daukacin al'umma da su bada hadin kai da goyon baya ga Kwamitocin domin a samu nasara.

     Babban Kwamitin na jiha wanda ke karkashin jagoracin Malam Halilu Musa Kofar - Bai, na da wakilan masu martaba Sarakunan Katsina da Daura, da wakilan Kungiyoyin Izala da Darika, da Kungiyoyin farar hula da Dr Bashir Ruwangodiya da Dr Ahmad Filin Samji da PPS, Abdullahi Aliyu Turaji da shugaba da Sakataren Jam'iyyar APC na jiha da Imam Samu Magaji Bakori.

      A jawabinsa, shugaban Kwamitin na jiha, Malam Halilu Musa Kofar- Bai, ya yi godiya ga Allah da yaba ma Gwamna Dikko Umaru Radda akan kirkiro da wannan shiri a lokacin al'umma ke cikin mawuyacin hali. Ya kuma yi fatar cewa za a sanya ido a ga abinda shi da daukacin abokan aikinsa za su aiwatar.

Abdullahi Aliyu Yar'adua,
Director Press A Madadin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *