Majalisa za ta binciki Emefiele kan baiwa Buhari bashin tiriliyan 30

top-news

Majalisar Dattawan Nijeriya ta sanar da cewa za ta gayyaci tsohon gwamnan babban bankin ƙasar nan, CBN, Godwin Emefiele domin ya amsa tambayoyi kan bashin Naira tiriliyan 30 da ya baiwa tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari lokacin yana jagorantar bankin, idan gwamnan bankin na yanzu ya kasa yi mata cikakken bayani kan kuɗin.

Shugaban kwamitin kula da bashin da CBN ke baiwa gwamantin tarayya da ake kira 'Ways and Means' Sanata Jibrin Isah daga jihar Kogi ne ya sanar da matakin gayyatar a lokacin da jami'an CBN, waɗanda mataimakin gwamnan bankin ya jagoranta suka bayyana gaban kwamitin a Abuja domin amsa tambayoyi.

Tuni dama Majalisar Dattawan ta kafa wani ƙaramin kwamiti da zai binciki bashin na 'Ways and Means' na Naira tiriliyan 30 da CBN ya baiwa gwamantin tsohon shugaban ƙasar.

An kuma ɗorawa kwamitin alhakin bincikar shirin bada tallafin kuɗi ga mutane ƙaramin ƙarfi na Anchor Borrower a zamanin Buhari.

'Ways and Means' dai bashi ne da CBN ke baiwa gwamantin tarayya domin cike giɓin kasafin kuɗi da aka samu.

Da yake yiwa manema labarai ƙarin bayani bayan ganawar, Sanata Isah ya ce kwamitin ya gano cewa Emefiele ya amince da bashin a lokuta daban-daban cikin takardun bayanan da majalisar ta samu, wanda ta ce ya saɓawa doka.

A kwanakin baya ne Majalissar Dattawan ta sanar da ƙudurinta na bincikar bashin a furucin da Ministan Kuɗi da Tattalin arziƙi Wale Edun ya yi. 

An daɗe dai ana zargin wasu daga cikin muƙarraban gwamnatin Buhari da almundahana, kuma tuni aka fara bincikar wasu daga cikinsu, ciki har da tsohuwar ministar jinƙai, Sadiya Umar Farouq da gwamnan na CBN, Godwin Emefiele da kuma tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, Abdulrasheed Bawa.

Alfijir Radio 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *