Wasu Mutane Ɗauke Da Bindigu Sun Yi Garkuwa Da Ɗanjarida a Legas

top-news

Rahotanni sun bayyana cewa wasu mutane dauke da manyan  bindigu sun yi dirar mikiya a gidan Segun Abiodun  Olatunji, tsohon shugaban ofishin jaridar The PUNCH na Kaduna, a gidansa da ke Iyana Odo a unguwar Abule Egba a jihar Legas.

Abiodun wanda a yanzu babban edita ne na jaridar FirstNews, kuma a wata sanarwar da jaridar ta fitar a ranar  Asabar din da ta gabata, hukumar gudanarwar kafar yada labaran ta alakanta lamarin da wani labari na baya-bayan nan da jaridar ta FirstNews ta buga mai taken,

"Revealed: “Defence Chief running office like family business – Public Interest Lawyers”.

Labarin da ke da alaƙa da ofishin rundunar tsaro.

Sanarwar ta ce karin  wasu kafafen yaɗa labarai na yanar gizo  sun buga labarin.

Sanarwar ta kara da cewa  ta yiwu sace ɗan jaridar na da alaƙa da   wani rahoto mai taken 

EXCLUSIVE: How contractor, company stole N100bn, laundered funds for top govt officials – Investigation”. Wato labarin yadda dan kwangila da wani kamfani ya saci Naira biliyan 100bn, labarin da jaridar ta goge ta kuma janye shi daga baya.

 A cewar sanarwar, uwargidan ɗanjaridar , ta ce mutanen ɗauke da manyan bindigu da yawansu ya kai mutum goma sun isa gidansu ‘yan mintuna kadan bayan karfe 6 na yamma, suka tafi da mijinta ba  tare da bayyana inda za su  kai shi ba.

Ta ce  “Wasu ‘mutane ne  sanye da kakin soji sun kai goma (biyu cikinsu basa sanye da kayan soji, suna sanye da kayan guda ne,mutum  8 sanye da kayan soji,  amma dukkansu dauke da makamai) sun isa gidanmu da ke titin Dauda Oriyomi, Iyana Odo  a unguwar Abule Egba a jihar Legas, suka tafi da  mijina".

Ta ce mijin nata yayi ta maimaita cewa, su faɗa masa laifinsa, su kuma faɗa masa inda zasu tafi da shi, amma suka ƙi faɗa masa.

Zuwa lokacin haɗa wannan rahoton babu ɗoriyar Ɗanjaridan sama da kwanaki biyar da faruwar lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *