Ƙarin kasafin kuɗi ya halasta a doka - Ministan kasafin kuɗi Atiku Bagudu

top-news

Ministan kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziƙi Sanata Atiku Bagudu ya ce majalisar dokokin Nijeriya bata karya wata doka ba bayan ta yi ƙari a cikin kasafin kuɗin 2024.

Da yake magana da manema labarai ranar Alhamis a Abuja ya ce tun shekarar 1999 ne ya zama al'ada ga majalisar dokoki, inda ta ke yin ƙari cikin kasafin kuɗi domin gudanar da wasu ayyuka na musamman a wasu mazaɓu, wanda hakan ke sa kasafin kuɗin ya ƙaru daga wanda shugaban ƙasa ya gabatarwa majalisa ta amince da shi tun da farko.

A baya bayan nan dai shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya yi shuhura a kafafen watsa labarai bayan zargin da aka yi masa cewar majalisar ta yi ƙarin kasafin kuɗi da Naira biliyan 3.7, inda jam'iyyar PDP mai adawa ta riƙa kiran ya yi murabus.

Sanata Abdul Ningi da ya fito daga jihar Bauchi ne ya fara tayar da batun ƙara kasafin kuɗin, wanda ya sa majalisar ta dakatar da shi tsawon wata uku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *