Har Yanzu Ba'a Ga Mannir Attiku Lamido mataimakin Shugaban Kungiyar Miyatti Allah Ta Kasa Ba.
- Katsina City News
- 31 Aug, 2023
- 762
A cikin wata tattaunawa da wakilin DW hausa a jahar Katsina Yusuf Ibrahim Jirgaba ya yi da iyalan Shugaban kungiyar domin ya ji ta bakin su game da halin da ake ciki sun nuna cewa sun shiga hali na bakin ciki da damuwa kasantuwar batar maigidansu sun kuma nuna takaicin su game da rashin zuwan daya daga cikin yayan kungiyar miyatti Allah domin yi masu jaje ko kawo masu taimako game da halin da suke ciki.
Aliyu Dabo kakakin kungiyar ya nuna takaicin shi akan halin da ake ciki na rashin ganin mataimakin Shugaban kungiyar miyatti Allah da kuma rashin samun wani labari game da shi, ya nuna hanyoyi da yawa wadanda ke sa mutane na bace wa. Ya ce mutane na bacewa ne ko an kashe su, wasu su kan bata ta dalilin ko sunyi gudu ne domin su tsira da rayuwar su, wasu kuma ta dalilin kama su da a ke yi ba tare da sanin iyalan su ba,
Mannir Atiko Lamido na daya daga cikin wadanda suka bada gudummuwa wajen shiga tsakani lokacin da akayi sasanci tsakanin gwamnatin jihar Katsina da yan bindiga a wancan lokacin kuma ya bata kimanin watanni ukku da suka wuce.