FACEBOOK 2004: A Rana Mai Kamar Ta Yau 4 Ga Watan Fabrairu 2004 Facebook , babban shafin sada zumunta na yanar gizo, Mark Zuckerberg da Eduardo Saverin suka kafa.
- Katsina City News
- 04 Feb, 2024
- 329
Dandalin Facebook
A ranar 4 ga Fabrairu, 2004, wani dalibi na biyu na Harvard mai suna Mark Zuckerberg ya ƙaddamar da Facebook , gidan yanar gizon da ya gina don haɗa ɗaliban Harvard da juna.
Zuckerberg ne ya kafa shafin sadarwa ta Facebook a ƙasar Amurka a shekara ta 2004.
An dai kafa shafin sadarwa ta Facebook ne a Ranar 4 ga watan fabairun shekara ta 2004 a ƙasar Amurka. Kuma wasu matasa uku wato Mark Zuckerberg da Chris Hughes da kuma Moskovitz ne suka ƙirkiro shafin a wannan shekarar. Wanda dai akace ya jagoranci kafa shafin na Facebook tsakanin matasan dai shine Mark Moskovitz ɗan shekaru 23 a duniya dake karatun Sanin halayan ɗan Adam wato Psychology, a lokacin da yake ɗalibta a jami'ar Harvard dake ƙasar ta Amurka domin amfanin ɗaliban jami'ar
Kafin kace kwabo wannan shafi ya samu ƙarɓuwa wajen sauran ɗalibai kimanin 1200 na jami'ar ta Harvard. Kuma cikin wata guda rabin ɗaliban dake karatun ƙaramin digiri na jami'ar sunyi rajista da shafin na Facebook. Haka dai wannan shafi ya rinƙa samun karɓuwa daga ɗalibai daga wannan jami'a zuwa wancan.
A shekarar 2005 ne kuma aka yiwa shafin rajista a matsayin facebook.com akan kuɗi Dalar Amirka dubu ɗari biyu. A watan satumban shekara ta 2005 kuma shafin na facebook ya isa ƙasar Birtaniya kafin zuwa sauran ƙasashen duniya. Kuma kyauta ne dai ake rajistan shafin na facebook.
Amma kuma don gane da hanyoyin samun kuɗi kuwa. Shafin wanda ya zama kamfanin na samun kuɗaɗen sa ne daga tallace tallace da manyan kanfanoni da ƙanana keyi domin sayar da hajar su ga masu anfani da shafin ta facebook. Yanzu dai kanfanin da aka fara da Dalar Amurka dubu ɗari biyu, a Shekarar 2010 kanfanonin sadarwa irin su Google da Yahoo sun taya shi akan kuɗi Dala biliyan 2, wanda kuma Mr. Zuckerberg yace albarka.
A shekarar 2004 an fara wata shari'a tsakanin Zuckerberg da kuma wasu masu mallakan kanfanin yanar sadarwa ta Connect U, wa'yanda ke zargin Zuckerberg da sace basirar kanfanin su, a lokacin da suka nemeshi daya shirya masu tsarukan shafin sadarwan su, a matsayin sa na kwararre a harkar na'ura mai ƙwaƙwalwa a lokacin da dukkannin su ke ɗalibta a jami'ar ta Harvard koda yake tuni kotu tayi watsi da ƙarar a sabili da rashin cikakkiyar shaida a shekarar 2007. Kuma kamar yadda wani shafin sadarwa shima na Wekepidia ta bayar yanzu haka dai akwai miliyoyin jama'a dake anfani da shafin ta Facebook da yawan su ya haura Biliyan 2 a duniya.
Meta
A Watan Oktoba 2021 ne Kamfanin Facebook ya sanar da cewa zai sauya sunan kamfanin da ke rike da shi zuwa Meta, a wani sabon salo da ya zo a daidai lokacin da kamfanin ke fuskantar matsalolin hulda da jama’a.
Masu amfani da Facebook nawa ne a cikin 2022?
2.934 biliyan
Ga abin da sabbin bayanai suka gaya mana: Adadin masu amfani da Facebook a duniya (masu amfani da shi a kowane wata): biliyan 2.934 (Yuli 2022) Yawan mutanen da ke amfani da Facebook kowace rana (DAU): biliyan 1.968 (Yuli 2022)
Masu amfani da Facebook nawa ne a Najeriya 2022?
kusan masu amfani da Facebook miliyan 28
Ya zuwa Disamba 2022, akwai kusan masu amfani da Facebook miliyan 28 a Najeriya, wanda ke da kashi 12.7 na yawan jama'ar kasar Gabaɗaya, kashi 34.1 cikin ɗari na masu amfani da Facebook suna tsakanin shekaru 25 zuwa 34, wanda hakan ya sa wannan rukunin shekarun ya zama mafi yawan masu amfani a cikin ƙasar, sai kuma masu shekaru 18 zuwa 24.