Gwamnatin Jihar Katsina Ta Fara Binciken Badakalar Filaye A Kusa da Kasuwar Mako ta Bakori
- Katsina City News
- 22 Jan, 2024
- 574
Zaharddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Gwamnatin jihar Katsina ta samu cikakken rahoto da ke bayani kan zargin badakalar filaye a kusa da kasuwar mako-mako ta Bakori, wanda ke da alaka da jami’an karamar hukumar Bakori. Dangane da wadannan zarge-zarge Gwamna Malam Dikko Umaru Radda Ph.D, ya dauki matakin gaggawa.
Gwamnan ya umurci Hukumar Kula da Ma’aikatun Kananan Hukumomi, da ta gaggauta magance lamarin.
Umarnin sun hada da gudanar da bincike cikin gaggawa kan zarge-zargen, tantance jami’an da abin ya shafa, aiwatar da matakan ladabtarwa da suka dace, da kuma gabatar da rahoton gaggawa ga Gwamna tare da shawarwari, idan ya cancanta.
Ana kallon matakin a matsayin wani shiri na gwamnatin jihar Katsina na tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin gudanar da kananan hukumomi. Abdullahi Aliyu Yar’adua, a madadin sakataren gwamnatin jihar Katsina ya sanya hannu a sanarwar, inda ya jaddada kudirin hukumomin jihar na magance zarge-zargen da ake yi cikin gaggawa.