KADIRI ABDU YA KAFA TARIHI A KOKOWAR JANHURIYAR NIJAR.
- Katsina City News
- 01 Jan, 2024
- 821
Ɗan kokowa mai suna Kadiri Abdu wanda aka fi sani da Issaka Issaka ya kafa tarihi a wasan kokowar gargajiya na Janhuriyar Nijar inda ya lashe takobi karo na shida, bayan ya kada Sule Mati.
A yau asabar 31-12-2023 aka kammala kwamɓalar kokowar gargajiya karo na 43 a birnin Agadas na Janhuriyar Nijar. Kafin karawa tsakanin waɗanda suka kai fagen ƙarshe, saida aka fafata domin neman gurbin na 3 da na 4, inda Nura Hassan ya kada Abba Ibrahim, Wanda ya ba Nura Hassan damar zama na 3, shi Kuma Abba ya zamo na 4 a wannan gasa ta bana.
Daga nan aka gayyaci mawaƙa da makaɗa domin nishaɗantar da ƴan kallo, sannan aka bada kyaututtuka ga waɗanda suka nuna bajinta ta musammun.
Sai aka gayyaci zaƙaƙuran yan kokowar da suka rage tsaye (watau waɗanda baa kada su ba) Kadiri Abdu, wanda ake kira Issaka Issaka wanda ya fito daga jihar Dosso, sai abokin karawar shi daga jihar Maraɗi Sule Mati. Sun fafata anyi turmin farko (minri biyar) babu kaye, bayan hutun minti biyu suka sake cigaba da fatawa inda ana gab da a sake tafiya wani hutun Kadiri Abdu ya samu sa'a yayi kaye, wanda wannan ya bashi damar lashe takobi karo na shida, shi kuma abokin karawar shi Sule Mati ya zo na biyu a wannan kwamɓalar kokowa ta bana.
Dama dai duk ƙarshen shekara akan gudanar da wannan gasar gargajiya a ƙasar wanda wannan shine karo na 43, ana aiwatar da shi.