Aliyu Ilu Barde a Bisa Jagorancin kungiyar Ibrahim Kabir Masari ta raba Kayan Abinci ga Mabuƙa a Katsina.
- Katsina City News
- 28 Aug, 2023
- 1159
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A ranar Litinin kungiyar da tayi fafutukar yaƙin neman zaɓen Dikko Radda na Katsina a matsayin Gwamna, da Shugaban ƙasar Najeriya Bola Ahamed Tinubu, mai suna "Asiwaju Gwagware gida-gida Initiative" ta raba kayan Abinci ga Al'umar Unguwar Tigirmis da Barhim a garin Katsina.
Kungiyar bisa Tallafin Matashin Dansiyasa Hon. Aliyu Ilu Barde ta yi lura da halin da al'umma suke ciki, inda suka shirya rabon kayan abinci, Masara da Shinkafa a Unguwannin Mabukata domin rage Raɗaɗin rayuwa.
A ranar Litinin kungiyar da 'ya'yanta suka shiga Unguwannin domin rabon kayan inda Al'umma suka tuɗaɗo daga ko ina a cikin yankunan domin amsar nasu rabon.
Da yake bayani a madadin mai unguwa, Malam Ilyasu ya bayyana jin dadi da godiya bisa wannan abin Alkhairi da aka kawo masu, yace sunji dadi an basu abinda akafi bukata a daidai lokacin da al'umma suke cikin wata lalura ta bukatar, a karshe yayi kira ga masu hannu da shuni da suyi koyi da Hon. Aliyu Ilu Barde domin su shiga cikin ladar da Allah kadai yasan irinta.
Tun da farko Wakilin Hon. Ali Barde a wajen rabon kayan abincin Malam Jamilu Labour ya bayyana makasudin zuwansu inda ya nemi addu'a da fatan Alkhairi ga dukkanin wanda Allah ya cida, kuma ya bayyana cewa wannan rabon kayan abinci zaici gaba domin a daidai irin wannan lokaci babu abinda al'umma sukafi bukata sai irin wannan tallafin.
Kungiyar ta Asiwaju ta saba rabon kayayyakin amfani ga jama'a. Ko a shekarar bara cikin yanayi na sanyi kungiyar ta raba Barguna, tabarmi da Butoci hadda shaddodi ga Makarantun tsangaya a kananan hukumomi 34 na jihar Katsina, kungiyar ta sake bada tallafi ga mata masu juna biyu na kayan haihuwa a ƙanan hukumomin jihar Katsina, inda daga bisani kuma ta tallafawa 'yan gudun hijira da marasa karfi da Magunguna a ƙanan hukumomin da matsalar rashin tsaro ta shafa.