Majalisar Dokokin jihar Katsina ta Tattauna akan Dokar da hana Macen da Mijinta ya Mutu Zuwa Aiki sai ta gama Idda
- Katsina City News
- 28 Aug, 2023
- 748
Kakakin Majalissar Dokoki ta Jihar Katsina, Rt. Hon Nasir Yahaya ya Jagoranci zaman Majalissa na yau Litinin 28-Augusta-2023. Inda aka tattauna akan Muhimman Batutuwa guda 2.
1- Na farko shine Kudiri akan Ƙir-Ƙirar hutu ga Mata Ma'aikatan Gwamnati wanda Allah ya yiwa Mazajensu Rasuwa, domin su samu damar yin Iddah kamar yadda Addinin Muslunci ya Hukuntar, Idan Mace Mijinta ya Rasu ba zata ƙara fitowa daga gidanta na Aure ba, har saita gama Iddah, inba tare da wani Cikakken Dalili ba
Kasancewar shi wannan Hutun babu shi a cikin Kundun Tsarin aikin Gwamnati na Jihar Katsina (Civil Service) yanzu ne Majalissar Dokoki ta Ƙudiri aniyar Ƙir-ƙirar Hutun, domin Mata wanda Allah ya yiwa Mazajensu Rasuwa su samu cikakken Lokacin da zasu gudanar da Ibadarsu.
-Hon. Shamsudeen Abubakar Dabai (Shugaban Masu Rinjaye)
2- Ƙudiri na Biyu shine. Kiran Gaugawa zuwa ga Bangaren Zartaswa da su taimaka su amshi Makarantar Jeka ka Dawo ta Sakandire ta garin Taramnawa. Wadda Al'ummar garin Taramnawa ne suka Gina ta a shekara ta 2017, a Karamar Hukumar Baure. Al'ummar wannan Gari suke daukar nauyin Makarantar da Al-jihunsu, tun daga lokacin da aka Gina ta har zuwa yanzu. (Community Secondary school Taramnawa)
Saboda Hali na yau da gobe da wani yanayi da Talakawa suka shiga ta Dalilin cire Tallafin man Fetur da Gwamnatin Tarayya tayi, aka kira Bangaren Zartaswa dasu taimaka su amshi Makarantar ta koma Ƙarkashin Kulawarsu domin a Kaucewa lalacewa ko Rushewar Makarantar.
Hon Suraja Umar (Tafidan Babban Mutum)
Kakakin Majalissa da sauran Abokin aikin sa suka aminta da wannan Kudiri guda 2 da aka Gabatar, inda Kakakin Majalissa ya bada Umarnin a tura shi zuwa ga Bangaren Zartaswa domin suyi duba akai.
Dalhat Daura
SSA Media and Publicity
28/08/2023.