TARON MANE MA LABARAI NA CIKAR KISAN KIYASHIN ZARIA SHEKARU 8 A ABUJA
- Katsina City News
- 12 Dec, 2023
- 459
Yau Talata ne rana ta farko na taron tinawa da kisan kiyashin Zaria karo na 8 a Abuja, taron wanda zai gudana tsawon kwanaki 5 anan Abuja birnin tarayyar Najeriya.
Harkar Musulunci ƙarƙashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yau Talata, ta fara gudanar da taron cikar shekaru 8 da kisan kiyashin Zaria wato #ZariaMassacre, taron wanda a bana ta shirya shi tsawon kwanaki 5.
A yau Talata rana ta farko an fara taron ne da gabatar da taron mane ma labarai (press conference), wanda aka gayyaci ƴan jaridu da masana a fannoni daban daban suka halarci taron, anyi wannan taro ne a cikin garin Abuja a wani ɗakin taro dake Savannah Sweet Area 3 Garki Abuja.
Prof. Dauda Nalado ya gabatar da karanta takardar mane ma labarai na tinawa da kisan kiyashin Zaria karo na 8, takardar wacce take dauke da bayanin yadda harin ya faru ƙarƙashin jagorancin Buhari da El-Rufai da Burtai. Har wala yau takardar ta ci gaba nuna jaddada goyon bayan harkar musulunci akan al'ummar Falasdinu.
Prof. Dauda Nalado ya ci gaba da karanto cewa harkar musulunci tayi Allah wadai da kisan musulmi a Tudun Maulidi (Biri), wanda irin kisan kiyashin da sojoji sukayi a Zaria irinsa sukayi a Tudun Biri suka kira hakan da kuskure kuma ba gaskiya bane.
Daga karshe wasu ba'adin mahalarta taron sunyi tambayoyi an basu amsa, sannan Sheikh Abu-Summaya Abuja ya rufe taron da addu'a, wannan ya kawo karshen taron a rana ta farko sai kuma gobe za'a ci gaba a rana ta Biyu.
-Asperger
-Isa Charis
-Ali Sajjad Ibn Tahir
12/December/2023