GWAMNA LAWAL YA HALARCI TARON ZUBA JARI NA AFREXIM A ƘASAR KENYA, YA CE JIHAR ZAMFARA NA BUƘATAR HAƊIN GWIWA TA GASKIYA MAI ƘARFI
- Katsina City News
- 27 Nov, 2024
- 90
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na mayar da hankali wajen lalubo hanyoyin haɗin gwiwar ci gaba na gaskiya da adalci da za su amfani zamantakewa da tattalin arzikin jihar.
Gwamnan ya wakilci Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya, kuma ya kasance babban baƙo a taron ƙara wa juna sani na Haɗin Gwiwa na Ƙasashen Afirka karo na huɗu, wanda aka gudanar ranar Litinin a otel ɗin Swiss Grand Royal da ke garin Kisumu ta ƙasar Kenya.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa, taron da aka fara daga ranar 25 zuwa 27 ga watan Nuwamba, Shugaban Ƙasar Kenya, Dr. Williams Ruto ne ya buɗe taron.
Sanarwar ta ƙara da cewa, taken taron na AfsNET shi ne "Yin amfani da AfCFTA don Samun Ɗorewar Cinikayya da Zuba Jari: Hanyar Ci Gaba ga Ƙasashen Afirka."
Gwamna Lawal, wanda ke gabatar da saƙon fatan alheri a madadin Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya, ya ce taken taron na AfsNET na bana ya yi daidai da muradun ci gaban gwamnatocin ƙasashen Afirka. "Taron na ƙalubalantar mu da mu daidaita dabarunmu da albarkatunmu don buɗe damar kawo sauyi a harkar Cinikiyyar Ta Gaskiya d Adalci A Afirka (AfCFTA).
“A Nijeriya, mun fahimci muhimmiyar rawar da ƙananan gwamnatocin ƙasashe ke takawa wajen tafiyar da harkokin kasuwanci, zuba jari, da ci gaban tattalin arziki. Jihohinmu 36 cibiyoyi ne na tattalin arziki daban-daban, kowannensu yana da rawar da yake takawa ta musamman da ke ba da gudunmawa ga tattalin arzikin ƙasa.
“Ana iya ganin babban misalin hakan a shirin Agro-Allied Industrial Zone ta Jihar Kaduna, shirin haɗin gwiwar gwamnati da ɗaiɗaikun jama'a da aka tsara don inganta noma tare da sarrafa anganin gona don fitarwa zuwa waje.
"Wannan aikin yana nuna yadda masu mulki za su iya amfani da albarkatun cikin gida da kuma tsarin AfCFTA don haɓaka ƙimar kasuwanci da faɗaɗa damar kasuwanci a duk faɗin Afirka. Hakazalika, yankin AfCFTA na Lekki ya zama abin koyi na samar da masana'antu da kuma jawo hannun jari kai tsaye daga ƙetare a jihar Legas. "
A wajen taron tattaunawa kan samar da mafita mai ɗorewa ga ci gaban yankin Afirka, Gwamna Lawal ya bayyana cewa, haɗin gwiwa ne zai kawo daidaito a bangaren ci gaban tattalin arziki.
“A matsayina na gwamna a yankin Arewa maso Yamma na Nijeriya, tare da haɗin gwiwar wasu gwamnoni shida, mun ƙirƙiro Ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma don bayyanawa tare da daidaita manufofin da za su samar da haɗin kan yankin don samun ci gaba mai ɗorewa. Wannan ya riga ya fara samar da sakamakon mai kyau a yankin.
Dangane da batun tsaro, Gwamna Lawal ya jaddada cewa, in ba tare da ingantaccen tsarin muhalli ba, gwamnatoci ba za su iya samar da ayyukan jin daɗin jama'a yadda ya kamata ba kamar ilimi, kiwon lafiya, daidaiton jinsi, kawar da rashin daidaito, da samar da ayyukan dogaro da kai ga maau ƙaramin ƙarfi, waɗanda su ne muhimman abubuwan da ake buƙata don ci gaba mai ɗorewa.
“Tsarin mulki ya taƙaita ƙarfin Gwamna ta fuskar samar da tsaro ga al’ummar da yake mulka; duk da haka, mun yi namijin ƙoƙari wajen ganin mun tabbatar da cewa muhallinmu ya kasance cikin kwanciyar hankali ta hanyar kafa Rundunar Kare Al'umma (CPG), wadda ta daƙile matsalar rashin tsaro da ake fuskanta kafin zuwan gwamnatina.”