Nijeriya Na Asarar Gangar Danyen Mai 400,000 A Kullum – NSA

top-news

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, ya ce har yanzu Nijeriya na asarar ganga 400,000 na danyen mai a kullum daga barayin gida da na waje duk da kokarin kawo karshen matsalar.

Ribadu ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci tawagar shugaban kasa don duba wuraren man fetur da iskar gas a Owaza da ke Abia da kuma Odogwa a karamar hukumar Etche ta jihar Ribas a ranar Asabar.

Ya ce ayyukan barayin man fetur da masu fasa bututun mai sun yi illa ga tattalin arzikin kasa kuma wani bangare ne da ke haddasa tsadar rayuwa a kasar.

“Abin takaici ne cewa wasu mutane kalilan ne za su sace dukiyarmu, kuma a cikin haka za su haifar da asara marar mai muni ga kasa ga jama’a.

“Nijeriya na da karfin samar da gangar danyen mai miliyan 2 a kullum, amma a halin yanzu muna samar da kasa da ganga miliyan 1.6 saboda sata da lalata bututun mai.

“Muna magana game da ganga 400,000 na danyen mai da ake barnatarwa tare da wasu masu aikata laifi da yi wa kasa zagon-kasa da tattalin arziki, shi yasa ba ma samun riba mai yawa,” Cewar Ribadu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *