Tarihin Unguwar Gambarawa
- Katsina City News
- 25 Aug, 2023
- 1077
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Unguwar Gambarawa tana bisa kan hanyar Kangiwa Zuwa Kofar Guga. Daga gabas ta yi iyaka da Bakin Kasuwa. Daga yamma ta yi iyaka da Filin Bugu. Daga arewa ta yi Iyaka da Malumma, daga kudu ta yi iyaka da unguwar Yari.
Gambarawa tana ɗaya daga cikin tsofaffin unguwannin Birnin Katsina. Tarihi ya nuna cewa an kafa ta tun lokacin Haɓe.
Unguwar ta samo sunanta ne daga wani Dangambara wanda ya zauna a wurin tare da iyalinsa shekaru aru aru da suka
wuce. Daga wannan suna ne mutane suka rika kiran wurin da Gambarawa', watau wurin da Dangambara yake da zama ko ya zauna.
A wani kaulin kuma, an ce unguwar ta samo sunanta ne daga wasu mutane da ake kira Wangarawa'.
wadannan mutane ance sun yi kaura ne daga tsofuwar daular Mali zuwa Birinin Katsina wajejen karni na goma sha bakwai. Daga cikinsu akwai Malamai da 'yan kasuwa. Lokacin da suka iso Birnin Katsina sun zauna ne a daidaı inda Gambarawa take.
Da farko mutane sun rika kiran wurin da suna Wangarawa'. Amma da tafiya ta yì tafiya, sai wannan suna ya canza zuwa 'Gambarawa.
Wasu kuma suna ganin cewa watakila Gambarawa ta samo sunanta ne daga kabilar Kambari, wadanda suka fara zama a wurin.
Da farko mai yiwuwa mutane sun rika kiran
wurin da suna Kambarawa, amma daga baya sunan ya canza ya koma "Gambarawa" Baya ga harkar kasuwanci, mutanen Gambarawa sun shahara a harkar malanta, watau koyar da ilimin addinin Musulunci. Cikin shahararrun Malaman da aka yi a zamanin da a wannan unguwa, akwai Malam Kisko. Wasu bayanan tarihi sun nuna cewa Shehu Mujaddadi Danfodio ya yi karatu a gidan Malam Kisko. Amna wannan bayanin ba a tabbatar da shi ba. Baya ga haka, Malam Kisko ya taimaka wa Sarakunan Katsina wajen bayar da fatawa musamman a fannin mulki da wasu matsalolin rayuwa na yau da kullum.
Baya ga Malam Kisko, akwai kuma wani shahararren Malami wanda ake kira Malam Muhammadu Batasaye, wanda asalinsa Bayammace ne. Da farko ya fara zama ne a garin Tasawa. Sa'annan daga baya ya yiwo kaura zuwa Birnin Katsina ya zauna a Gambarawa. Bayanai sun nuna cewa banda harkar koyarda ilimin addinin Musulunci, Malam Muhammadu ya kuma shahara wajen ilimin magungunan musulunci da ake kira Ɗibbun Nabawiy'.
Sauran mashahurran Malamai da aka yi a Gambarawa sun hada da Malam Abdulhamidu, da Malam Attahiru, da Malam Abdussalami, da Malam Shawai, da Malam Muhamman, da Malam Abdulkarim, da Malam Sani Malamin Makwayo, da Malam Abbas, da Malam Ibra, da Malam Hamisu, da Malam Babangida Abbas da Malam Iro na Habu da sauransu.
Akwai bayanai da ke nuna cewa kakar marigayi Sarkin Katsina, Alhaji Sir Usman Nagogo mai suna TaMalamai' an auro ta ne daga Gambarawa wadda ake dauka a matsayin 'Unguwar Malamai. Wannan ne ya sa akeyi wa Nagogo kirari da 'Jikan TaMalamai da Gidado'. Bugu da kari, tarihi ya kuma nuna cewa Gambarawa ita ce ta fara samar da limamai a tsofan masallacin Gobarau wanda aka gina a zamanin Sarkin Katsina Muhammadu Korau a karshen karni na goma sha biyar.
Daga cikin kayayyakin tarihi da ke a Gambarawa, akwai Kabarin Malam Kisko, da rijiyar lafiye, da rubuce-rubucen Tsaffin Malamai da Masallacin marigayi walin Katsina Alhaji Bello Kagara.
Rijiyar Lafiye tana nan a tsakiyar unguwar. Tarihi ya nuna cewa an gina ta kamar shekaru dari da hamsin da suka wuce. Rijiyar Lafiye tana da ban mamaki. A wani kaulin ance ba gina ta aka yi ba, amma ana zaune ne kawai sai akaga Kafin ka ce kwabo, sai aka ji rim! Kasa ta nisa.
Sai mutane suka rika tambaya lafiya? Abin mamaki sai kawai aka ga rijiya ta bayyana Babu kashe kudi, babu wahala, ba cas ba as, ga rijiya sai ɗibar ruwa.
Wasu kuma suna da ra'ayin cewa dama can a kwai ta, amma saboda halin yau da gobe shekaru aru-aru sai ta cike.
sai daga baya kuma ta sake dawowa kamar yadda ake sa ran dawowar wadansu rijiyoyin da suka cike ko aka cike su, an ce ko badin badade su ma za su dawo.
Daga cikin shahararrun yan kasuwa na Gambarawa akwai Alhaji Almu mahaifin Alhaji Abu Modibbo, da Alhaji Muhammadu Mannir da Alhaji Yahaya Dankıri da Sarkin Haya Alhaji Lawal da Alhaji Sani Namaska, da Alhaji Amadu Iliyasu da Alhaji Waziri Tunau, da Alhaji Yusha'u, da Alhaji Abubakar Modibbo, da Alhaji Idi Labari da Alhaji Bishir Dan Turai, da Alhaji Sama Ila Gambarawa, da Alhaji Shehu Mai Zare. Sauran sun hada da Alhaji Abdu Dankabo Maigoro, da Alhaji Nuhu Mai Kayan Yaji, da Alhaji Abulle Baban Iro Mashal, da Alhaji Almu. A wannan Unguwa ne akayi , Alhaji Bello Kagara
wannan unguwar ne aka yi su marigayi Walin Katsina Alhaji Muntari Bello, da
Alhaji Umaru Tamu na cikin Littafin Malam Bambadiya.