Nijar: ’Yan Ta’adda Sun Ƙona Motocin Kayan Abinci A Kan Iyakar Burkina Faso
- Katsina City News
- 24 Aug, 2023
- 687
’Yan ta’adda sun ƙona motocin dakon abinci sun harbe direban ɗaya daga cikin motocin da ke kokarin fitar da abinci daga Jamhuriyar Nijar.
Wasu da ake zargi ’yan ta’adda ne sun harbe direba dan kasar Ghana mai jan wata babbar motar dakon kaya a yayin da yake kokarin fitar da abinci daga Jamhuriyar Nijar.
Maharan sun kuma ƙona da dama daga cikin manyan motoci, jireban motar da suka harba kuma na jinya a wata cibiyar lafiya a Nijar.
Ya kasance a cikin rukunin direbobin da suka zaɓi hanyar Burkina Faso don kai kayan abinci masu mahimmanci zuwa Ghana.
Matakin dai ya biyo bayan rufe iyakokin kasar ta Nijar ne sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi, lamarin da ya janyo takun saka da ƙungiyar ECOWAS.
Rahotanni na cewa, direbobin sun yi yunkurin wuce iyakar Burkina Faso ne da kansu, bayan da suka jira a yi musu rakiya.
Rikicin da ya biyo bayan hambarar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum da sojoji suka yi a baya-bayan nan ya jefa Nijar cikin wani yanayi na rashin tabbas.
Wannan hargitsin siyasa ya yi matukar kawo cikas ga zirga-zirgar kayayyaki da na jama’a zuwa ko kuma fita daga kasar da ke yammacin Afirka.