ƳAN BINDIGA SUN KAI HARI KATSALLE TA BATSARI

top-news

Misbahu Ahmad 
@ Katsina Times 

A daren jiya talata 21-08-2023 ƴan bindiga suka kai hari wani ƙauye mai suna Katsualle dake cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina. Ƙauyen yana kusa da shataletalen ziro ziro da unguwar magama cikin garin Batsari akan hanyar Jibiya, kusa da mazaunin jamian sojoji. 
Sun saɗaɗo sun faɗa gidajen mutane ba tare da sunyi harbi ba, suka ɗauki mata biyar. Lokacin da aka farga an sanar ma sojoji, inda suka bisu har yammacin Gobirawa amma basu same su ba sai dai mutane sunji ƙarar rurin bindigu kamar ana fasa dutse da nakiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Abdulkareem AK Ibrahim

Allah ya kawo mana karshen wannan musifa ya Kuma tona asirin duk masu taimaka ma wannan miyagun mutanen ameen, su Kuma da aka dauka ya Allah ka kubutar dasu cikin koshin lafiya ameen.