Dangantaka tsakanin Karim Benzema da kocin Al-Ittihad Nuno Espírito Santo ta yi tsami...

top-news

Kociyan yana ganin Benzema bai dace da salon wasansa ba kuma ya ce bai taba nemansa ya koma kungiyar ba!

 Karim Benzema ya amince da Saad Al-Ladidh, wanda shine ke hulɗa da kwantiragi kuma shine wanda ya iya shawo kan Benzema ya koma Saudi Arabia, Al-Ladidh ya ce bai ji dadin halin Nuno Espírito ba, Saboda baya kula da kwarewar dan wasan. 

 Benzema ya nemi a ba shi kambum kyaftin din kungiyar amma kociyan ya ba Romarinho, don haka dan kasar Faransa bai zo atisaye a safiyar yau ba. 

  Nuno Espírito Santo ya soki Al-Ittihad cewa Benzema bai dace da salon wasansa ba kuma ya ce bai taba neman sa a kungiyar ba. 

  Hukumar kula da Al-Ittihad ta yi wa kocin dan kasar Portugal barazanar soke kwantiraginsa idan Benzema bai dawo atisaye ba.  (Moyen-Orient)

© Fagen Wasanni

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *