Kudaden Da Ministocin Tinubu Za Su Lakume
- Katsina City News
- 23 Aug, 2023
- 650
Ana ba wa minista miliyan N16.20 na gida; kudin mota N8m, kudin kayan daki miliyan 6, da kudin sallama N6m
Ministocin da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya rantsar za su lakume akalla Naira biliyan 8.6 a matsayin albashi da alawus-alawus a tsawon shekara hudu.
Akwai kuma yiwuwar kudaden su iya fi hakan, kasancewar hukumar tsara albashi ta kasa na kokarin fitar da sabon albashin ma’aikata da ta yi gyaran fuska.
Masana na ganin kudaden da za a kashe wa ministocin sun yi yawa, sun kuma saba da alkawarin Tinubu na rage yawan kudaden tafiyar da gwamnati.
Suna zargin yawan ministoci da hadiman gwamnatin Tinubu zai kara mata nauyi kuma zai kara jefa miliyoyin ’yan Najeriya cikin matsi, sakamakon makudan kudaden da za a rika kashewa na gudanar da gwamnati.
Ministoci 48 da Shugaba Tinubu ya rantsar shi ne adadi mafi yawa tun bayan dawowar Najeriya kan tsarin dimokuradiyya shekarar 1999.
Kafin shi, magabacinsa, Muhammadu Buhari ya nada ministoci 42, Goodluck Jonathan 33, Umaru Musa Yar’Adua 39, sai Olusegun Obasanjo ministoci 42.
Abin da za a biya kowane minista
Albashi da alawus din ministocin zai kama Naira biliyan 13 a shekara hudu, amma banda alawus dinsu na tafiye-tafiye.
Don haka masana ke cewa lokaci kawai zai nuna yawan kudaden tafiye-tafiye da sabbin ministocin za su samu, la’akari da dabi’ar ’yan siyasar Najeriya ta yawan son zuwa kasashen waje.
Ministoci kan yi tafiyar aiki zuwa kasashen waje domin halartar taruka ko neman masu zuba jari a bangarorin da ke karkashin kulawarsu.
Albashin minista
Shafin hukumar tsara albashi ta kasa (RMFAC) ya nuna tsurar albashin minista a wata N650,135.99 ne, a shekara N7.801m ke nan.
Gundarin albashin minista dai a wata miliyan N2.03 ne; man motarsa miliyan N1.5; ma’aikacinsa N506,600; mai aikin gida N1,519,800; tarbar baki N911,880; zirga-zirga N607,920; sanya ido N405,280, sayen jarida N303,960.
Bayan haka akwai miliyan N16.20 na gida a duk shekara hudu; miliyan N6.079 na kayan daki; kudin sallama N6.079m; kudin hutu dubu N810 da kudin mota N8.1m.
Albashin da kowanne minista zai lakume ya kama Naira miliyan N31.2m a shekara hudu; na jimillar ministoci 48 kuma biliyan N1.497bn na tsawon shekara hudu.
Kowane minista kuma zai samu wani karin alawu na miliyan N37.28 a wata, wato dukkansu biliyan N1.785 a wata, ma’ana biliyan N7.142 a shekara hudu.