Hukumar Tarihi da Al'adu ta jihar Katsina ta Kira 'Yan Fim da Mawaƙa domin samar da tsari da zai ciyar da Jihar Katsina gaba.
- Katsina City News
- 22 Aug, 2023
- 1058
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
A ranar Talata 22 ga watan Agusta ne Hukumar Adana Kayan Tarihi da raya Al'adun gargajiya ta jihar Katsina bisa Jagorancin Dakta Aliyu Rabi'u Kurfi suka shirya wani taro na Fahimtar juna dan lalubo hanyoyin da za'a samar da ci-gaba a Masana'antar.
Taron da ya gudana a Babban Gidan na raya al'adu ta jihar Katsina wato (Katsina Open Air theater) dake hanyar zuwa Jibiya a cikin garin Katsina ya samu halartar kungiyoyin masu wasan Hausa, irinsu MOPPAN, Arewa Fim Makers, National Actors Guilds, Kungiyar Masu Wasan Kwaikwayo, (Na Yalli) Mawakan gargajiya da na Zamani da sauran masu ruwa da tsaki a wajen raya al'adu.
Da take jawabin Maraba, Babbar Sakatariyar hukumar ta bayyana Mawaƙa da 'Yan Film a matsayin Likitoci kuma Kanikawan Al'adu, tace sune Likitoci kuma har wayau sune Kanikawa, anan gidan ne ake feɗe Al'ada a gyara ta, kuma ayi kanikancinta. Tace don haka su lura kuma su gane muhimmancin da Baiwar da Allah yayi masu.
Dakta Aliyu Rabi'u Kurfi Babban Daraktan Ma'aikatar Tarihi da Al'adu ta jihar Katsina wanda bisa Jagorancinsa aka shirya taron yayi sharhi gami da Tambihi mai tsawo akan Muhimmancin 'Yan Film da Mawaƙa na gargajiya da na zamani a fagen Al'adu.
Sanan yaja hankalinsu game da iya baki da tsarkake sana'ar.
Dakta Kurfi yace "Wannan Ma'aikata da nake jagoranta ta shira tsaf domin kawo gyara da tsari gami da Dokokin da kowa zaiyi Farinci da haka," yace, Amma duka yanda muke so mu kawo gyara ba zamu samu yanda muke so na cimma guri ba sai da hadin kanku."
Dakta yace "wannan zama ne na kusanni insan ku, a matsayina na Bako, amma zan biku daya bayan daya, kungiya kungiya in tattauna daku, muji shawara da kuma bukatunku da zamu iya duba yanda za a iya aiwatar da su."
Dakta Kurfi yace Kofarsa a bude take ga duk wani da yake so ya tattauna dashi akan hanyar kawo gyara domin bunkasa al'adun Hausawa.
A karshe an bawa wakilan kungiyoyi dama da su bayyana wasu daga cikin Ƙorafe-ƙorafe da kuma shawarar da zata amfani hukumar inda shugaban hukumar ya bayyana cewa zasu tattara dukkanin bayanansu domin zaunawa da Kwamishinan ma'aikatarsa da kuma Gwamnatin jihar Katsina domin ganin an aiwatar dasu.
Wannan taron shine na ukku da aka shirya a gidan na raya al'adu, wanda a farko Shugaban ya kira kungiyar 'Yan Dambe, da Ƙungiyoyin masu sana'ar Gargajiya, Masunta, Masaka, Makera, wanzamai, badukai, da masu sana'ar Magungunan Gargajiya, wanda ake saran ganawa da malamai na Addini a nan gaba domin a fahimci juna inji shugaban.