KatsinaTimes | 22 Nov 2025
Hukumar Kula da Hanyoyi ta Tarayya (FRSC) tare da haɗin gwiwar Kwapda’as Road Safety Demand (KRSD) sun shirya taron kasa da kasa na kwanaki biyu mai taken “International Road Crash Victims Africa Conference” a Abuja, Najeriya.
Taron ya tattaro shugabanni da masu ruwa da tsaki daga kasashen duniya da nahiyar Afirka domin tattauna batutuwan tsaro a hanyoyi, matakan gaggawa, da tallafawa wadanda hatsari ya shafa.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume, a wajen taron.
Manyan baki da suka halarci taron sun haɗa da Babban Joji na Tarayya, Babbar Alkalin Kotun Ƙoli ta Ƙasa Hajiya Binta Murtala Nyako, Sanata Adam Oshiomhole, Shugaban Hukumar EFCC, da shugabannin hukumomin tsaron hanyoyi daga ƙasashe 17 na Afirka, inda wasu daga cikinsu suka gabatar da kasidu masu alaka da taken taron.
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, Ph.D., CON, ya samu wakilcin Shugaban Hukumar KASSAROTA na Jihar Katsina, Major Garba Yahaya Rimi (Rtd), wanda ya samu rakiyar Sakataren Hukuma, Aminu Lawal Batsari; Kwamandan Hukumar na jiha, Dahiru Mani Bagiwa; Daraktan Kudi, Lawal Mamman Daura; da Jami’in Hulɗa da Jama’a, Abubakar Marwana Kofar Sauri.
A jawabin sa, Major Rimi ya ce taron ya samar da dandali mai sahihanci don tattaunawa, tuna abubuwan da suka faru, da aiki tare wajen tsaro a hanyoyi a nahiyar Afirka. Ya jaddada cewa Jihar Katsina za ta ci gaba da bin manufofi da ke kare rayuka da ƙarfafa tsarin kai daukin gaggawa.
Ya bayyana ci gaban da Hukumar KASSAROTA ta samu ƙarƙashin jagorancin Gwamna Radda, ciki har da ɗaukar ma’aikata 304 sabbi, wanda yasa jimillar ma’aikatan hukumar suka kai 400. Ya kuma bayyana cewa wayar da kan jama’a, aiwatar da doka akan daukar kaya ko mutanen da suka wuce kima a kan ababen hawa, da haɗin kai da al’umma sun taimaka wajen inganta dabi’un tuki da bin dokokin hanya.
Haka kuma, DG ya sanar da shirin Community Safety Volunteers na KASSAROTA, wanda zai horar da masu sa kai 3,610 (goma goma daga kowace mazaba daga cikin mazabu 361 na Jihar Katsina) domin bayar da taimakon gaggawa, haɗin kai a lamura masu bukatar agaji, da tallafin kare rayuwa na farko—shirin da nufin rage mace-mace sakamakon jinkirin matakin gaggawa.
Bugu da ƙari, ya gabatar da tsarin Katsina State Vehicle Identification and Database Management System (KASVID+), wani dandali na zamani da ke haɗa FRSC, KASSAROTA, da sauran hukumomin tsaro don inganta bin doka, lura da motoci, da yanke shawara bisa bayanan da aka tattara.
Ya bayyana cewa Jihar Katsina ta samu raguwar hatsarorin hanya da kashi 39% a shekarar 2025, yayin da Najeriya ta samu ƙaruwa da kashi 10.04% a matakin ƙasa. Ya danganta wannan nasara ne da ingantaccen tsarin gina sabbin hanyoyi fiye da kilomita 285, da gyare-gyare da kuma farfado da Hukumar Sufuri ta Jihar Katsina (KTSTA), wadda yanzu ta zama ɗaya daga cikin mafi inganci a Najeriya.
Major Rimi ya jaddada tabbacin gwamnati wajen samar da kulawar gaggawa ga wadanda hatsari ya shafa, musamman ma’aikata da iyalansu, ta hanyar shirin kiwon lafiya na Katsina State Contributory Health Care Scheme (KATCHIMA), domin samun magani ba tare da biyan kuɗi nan take ba.
Ya kammala jawabin sa da cewa Jihar Katsina ta shirya haɗin gwiwa da sauran ƙasashen Afirka don ƙarfafa hukumomi, inganta tsaron hanya, da gina tsarin sufuri mai aminci ga ɗan adam.
Sanarwa daga Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar KASSAROTA, Abubakar Marwana Kofar Sauri.