Rashin Kula da Al’umma: ‘Yan Ingawa Sun Zargi Hakiminsu da Sakaci da Harkokin Masarauta

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes09112025_101243_FB_IMG_1762683154460.jpg

Daga Wakilinmu, Katsina Times

Wasu mazauna Karamar Hukumar Ingawa a Jihar Katsina sun zargi Sarkin Fulanin Dambo, Alhaji Tukur Suleiman Dambo, da sakaci da al’amuran masarauta da rashin kusanci da jama’arsa tun bayan nadinsa a matsayin Hakimin Ingawa kusan shekaru shida da suka wuce.

A cewar jama’ar yankin, tun bayan da aka nada Alhaji Tukur Suleiman Dambo, bai taba yin zama da jama’arsa ko gudanar da taron masarauta ba, saboda kasancewarsa ma’aikaci a Legas, wanda ke hana shi gudanar da ayyukan da suka shafi jama’ar da yake jagoranta.

“Tun da aka nada shi, ba mu taba ganin Hakimi cikin al’umma ba. Duk wani ci gaba da ya kamata mu tattauna a masarauta, sai mu ji shi a wata masarauta daban,” inji wani mazaunin Ingawa da ya nemi a sakaya sunansa.

Haka kuma, wani dattijo mai suna Malam Umar ya bayyana cewa, masarautar Ingawa ta Da, tana da martaba da kusanci da talakawa, inda ya ce, “A da, Sarki da talakawansa suna tare da juna. Amma yanzu, da wuya ka samu wanda ya san Hakimin Ingawa cikakken sani.”

Malam Umar ya ci gaba da cewa, “Ya kamata a gyara tsarin da ke bai wa ma’aikatan gwamnati damar rike sarauta yayin da suke aiki, domin a doka ba a hada mukamai biyu. Idan mutum yana son rike sarauta, sai ya ajiye aikin gwamnati. Wannan zai kare mutuncin masarauta da tsarin gwamnati gaba ɗaya.”

Katsina Times ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Sarkin Fulanin Dambo ko wakilinsa kan wannan zargi, amma hakan bai samu ba. Duk da haka, wani daga cikin iyalan gidan Dambo, wanda ya nemi a boye sunansa, ya tabbatar da cewa akwai gaskiya cikin maganganun jama’a.

“Da za ka kawo jerin masu rike da sarauta a gaban Hakimin Ingawa, da yawa daga cikinsu bai san su da sunansu na asali ba, sai dai kadan. Amma a haka ya nada wani matashi da bai da gogewa, wanda ba ya iya kare mutuncin masarauta, a matsayin wakilinsa. Wannan abin takaici ne,” inji shi.

Masu ruwa da tsaki a yankin sun roki Masarautar Katsina da Gwamnatin Jihar Katsina da su duba lamarin domin kare martabar masarautar Ingawa da mutuncin masarautar Katsina gaba ɗaya.

Sun kuma bukaci gwamnatin jihar ta dawo da tsarin hana ma’aikatan gwamnati rike sarauta ta mulki, sai dai idan sun ajiye aikin gwamnati, domin kauce wa rikice-rikice da rage darajar sarauta a idon jama’a.

Masana a fannin tarihi da zamantakewa sun ce irin wannan yanayi na iya haifar da gibin mulki a tsakanin shugabanni da jama’a. Malam Isa Bala, mai nazarin harkokin masarautu, ya bayyana cewa, “Rashin kasancewa kusa da al’umma na rage daraja da tasirin sarauta a zukatan jama’a. Sarauta ba ta takaita ga suna da rawani kawai ba — tana bukatar hidima da kusanci.”

“Idan gwamnati ta ci gaba da barin ma’aikata su rike mukaman gargajiya, hakan na iya kawo ruɗani tsakanin tsarin gwamnati da tsarin gargajiya,” inji shi.

Lamarin Hakimin Ingawa ya sake bayyana matsalar da ke tattare da rike mukaman gargajiya da na gwamnati lokaci guda matsalar da masana ke ganin ta bukaci doka da tsari mai ƙarfi don kare mutuncin masarautu a Najeriya.

Follow Us