Kungiyar Shuwagabannin Makarantu Masu Zaman Kansu ta Kasa, Reshen jihar Katsina (NAPPS), ta bayyana godiyarta ga Gwamna Dikko Umaru Radda bisa amincewa da sake yin nazari kan wasu sabbin dokokin gudanar da makarantu masu zaman kansu da makarantun al'umma a jihar.
Wata sanarwar da shugaban ƙungiyar na jihar, Alh. Mansur Sani Jibia ya sanya wa hannu, ta ce gyaran fuskar da aka ma dokar zata kara daidaita aiyukan makarantu masu zaman kansu da makarantun al'umma don su cigaba da bada gudummawa ga inganta bangaren ilimi a jihar.
"Ƙungiyar Shuwagabannin Makarantu Masu Zaman Kansu, reshen Jihar Katsina, tana sanar da godiyarta da fatan alheri ga Gwamnan Jihar Katsina bisa kasancewarsa shugaba mai sauraron koken al'umma, mai tuntuba, kuma mai kulawa da halin da alumma ke ciki.
"Kungiyar NAPPS tana kuma yaba wa dukkan 'yan Majalisar Dokokin Jihar Katsina musamman Shugaban Majalisar, Rt. Hon. Nasir Yahya Daura, da Hon. Mustapha Yusuf Jibia, da kuma Sakataren Gwamnatin jihar, Alhaji Abdullahi Garba Faskari, da ofishinsa, bisa rawar da suka taka wajen gudanar da tattaunawar tsakanin ma'aikatar Ilimi ta da kungiyar NAPPS.
"Ƙungiyar tana yi wa mai girma Gwamna fatan alheri, da nasara, da kariya, da jagora a shugabancinsa domin daga martabar jihar Katsina zuwa mataki na gaba", in ji sanarwar.
Kungiyar ta NAPPS ta ce a shirye take ta yi da'a ga duk wasu dokoki da ƙa'idoji da aka shimfida wajen gudanar da makarantunsu, da kuma aiki tare da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki don ƙarfafa bangaren ilimi a jihar bisa tsarin cigaba na gwamnatin Malam Dikko Umaru Radda.