Katsina TIMES | Talata, 16 ga Satumba, 2025
Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina, Alhaji Bala Abu Musawa, ya yaba da kokarin Gwamna Dikko Umar Radda wajen magance matsalar tsaro a jihar, inda ya ce ko da yake ba a kawar da matsalar gaba ɗaya ba, amma akwai ci gaba da ake gani a wurare da dama.
Alhaji Musawa ya bayyana haka ne a lokacin da tawagar gwamnatin jihar tare da shugabannin jam’iyyar APC suka kai ziyara a wasu kananan hukumomi na shiyyar Katsina, domin tattaunawa da shugabannin jam’iyyar a matakin ƙananan hukumomi da mazabu.
Tawagar ta ziyarci kananan hukumomin Danmusa, Safana, Dutsinma da Kurfi, inda suka gana da shugabannin jam’iyyar APC a matakin ƙananan hukumomi da mazabu, da kuma masu aikin tunkarar jama’a da ake kira ‘yan tara-tara.
“Ba za mu ce an kawar da matsalar tsaro dari bisa dari ba, amma za mu iya cewa Gwamna Dikko Radda na yin iya bakin kokarinsa wajen ganin an kawo ƙarshen wannan matsala. A wasu garuruwa musamman inda aka cimma yarjejeniyar sulhu, an samu sauki sosai,” in ji Alhaji Musawa.
Ya bayyana cewa matsalar tsaro ta dade tana damun jihar tun kafin zuwan APC, amma ya bukaci jama’a da su ci gaba da goyon bayan gwamnati da kuma yin addu’a domin a samu nasarar kawo ƙarshen matsalar.
Musawa ya kuma bayyana cewa Gwamna Radda ya amince da ɗaukar sabbin masu taimaka a kananan hukumomi ta bangarori daban-daban har mutum hamsin 50, mata 10 da maza 40 – tare da kira ga shugabannin ƙananan hukumomi da su ma idan da dama su kara ga wadannan, su ɗauki masu taimaka masu kan harkokin sadarwa domin ƙarfafa tunkarar jama’a a.
A nasa jawabin, mai ba wa Gwamna shawara kan harkokin jam’iyya, Hon. Shafi’u Abdu Duwan, ya kaddamar da kwamitin da zai sabunta jerin shugabannin rumfuna da ‘yan tara-tara a mazabu, bisa la’akari da cewa wasu sun rasu ko kuma sun sauya jam’iyya.
Danmajalisar tarayya mai wakiltar Mashi/Dutsi a Majalisar Tarayya, Hon. Salisu Yusuf Majigiri, ya yi kira ga shugabannin jam’iyya da su mayar da hankali wajen shirin babban zabe mai zuwa domin tabbatar da nasarar jam’iyyar APC.
Shugabannin ƙananan hukumomin da suka yi jawabi sun nuna godiya ga jam’iyyar APC da kuma Gwamna Dikko Radda bisa irin gudummuwar da yake bayarwa musamman wajen inganta tsaro da ayyukan ci gaban al’umma a yankunan da ke fama da matsalar rashin tsaro.
A cikin tawagar akwai Hajiya Jamila Salman Mashi, shugabar mata ta jam’iyyar APC a jihar, Alhaji Yahaya Asasanta, Alhaji Babangida Shinkafi, Hon. Habibu Nakiya da sauran manyan jiga-jigan gwamnati da jam’iyyar APC a jihar Katsina.