Masana’antar Man Dangote Ta Sayi Danyen Mai Daga Kamfanin NNPC Na Naira Biliyan 11 a Watan Yuli

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes05092025_123755_-1x-1 (2).webp

KatsinaTimes Business Desk 

Masana’antar sarrafa man fetur ta Alhaji Aliko Dangote da ke Ibeju-Lekki, Jihar Legas, ta karɓi danyen mai na dala miliyan 7.2 (kimanin Naira biliyan 11.2) daga kamfanin NNPC a watan Yuli, karkashin tsarin naira-don-danye da gwamnati ta kafa.

Bayanan da NNPC ta gabatar wa kwamitin raba kudaden shiga na ƙasa (FAAC) sun nuna cewa wannan shi ne karo na farko da aka tabbatar da isar da danyen mai ga babban kamfanin bayan sake jaddada manufar nan ta naira-don-danye a farkon wannan shekarar.

Rahoton ya bayyana cewa NNPC ta sayar da gangar mai dubu 340 a watan Yuli da kudin da ya kai dala miliyan 22.5 (kimanin Naira biliyan 34.6). Cikin hakan, kamfanin Dangote ya karɓi gangar mai dubu 100 na Okwuibome, wanda kamfanin SEEPCO ya samar, ta hanyar jirgin Sonangol Kalandula.

Mai ɗauke da farashin dala 72.1 kowace ganga, jimillar kudin ta kai dala miliyan 7.21, wanda aka sauya a kan farashin Naira 1,553.27 ga kowace dala, ya zama Naira biliyan 11.2. Wannan ya kai kashi 32 cikin 100 na kudaden shiga da NNPC ta samu a watan.

Gwamnati ta ƙaddamar da tsarin naira-don-danye tun a watan Oktoba 2024, wanda ya wajabta wa NNPC sayar da danyen mai ga masana’antun cikin gida da naira maimakon dala. Manufar ta nufi rage matsin kasuwar kuɗin waje, tabbatar da isar da danyen mai ga gidajen sarrafawa a gida, da kuma rage dogaro da shigo da man fetur daga waje.

Sai dai a watan Maris, kamfanin Dangote ya dakatar da sayar da man da ya sarrafa a cikin gida da naira, yana mai cewa akwai matsala tsakanin kudaden shiga na naira da kudin danyen mai da ake saya da dala. Gwamnati daga baya ta sake tabbatar da manufar, tare da sanya Afreximbank a matsayin mai ba da shawara kan yadda ake ƙayyade farashin musayar kudi.

Masana sun bayyana cewa samun ci gaba wajen isar da danyen mai ga kamfanin Dangote na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da aikin wannan masana’anta, wacce take da ƙarfin sarrafa gangar mai har dubu 650 a rana – matata mafi girma a duniya guda ɗaya tilo.

A bangaren Najeriya kuwa, karkatar da danyen mai zuwa masana’antar Legas na daga cikin muhimman matakan rage makudan kuɗi da ake kashewa wajen shigo da man fetur. Sai dai har yanzu akwai tambayoyi kan adadin danyen man da za a ci gaba da baiwa kamfanin, tsarin tsadar da ake amfani da shi, da kuma iya gamsar da bukatun cikin gida tare da gogayya da man da ake shigowa da shi daga kasashen waje.

Follow Us