Sanata Ibrahim Ida ya jagoranci kwamitin da ya kammala aiki kan tarihi da al’adun gargajiya a jihar
A ranar Laraba, 23 ga Yuni, 2025, kwamitin da gwamnatin jihar Katsina ta kafa domin duba hanyoyin farfaɗo da muhimmancin wuraren tarihi da al’adun gargajiya a jihar, ya kammala aikinsa tare da miƙa cikakken rahoto ga sakataren gwamnatin jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Garba Faskari.
Kwamitin, wanda Sanata Ibrahim Ida (Wazirin Katsina) ke jagoranta, ya gudanar da bincike mai zurfi kan manyan cibiyoyi da abubuwan tarihi da suka shafi masarautun Katsina da Daura, da kuma al’adun gargajiya da suka haɗa da bukukuwan hawan sallah. Rahoton na ƙarshe ya ƙunshi shawarwari da dabarun da za su taimaka wajen farfaɗo da waɗannan wurare da kuma bunkasa al’adun jihar.
Sanata Ida, yayin gabatar da rahoton, ya bayyana cewa kwamitin ya ziyarci wuraren tarihi da dama tare da ganewa ido, da kuma yin tuntuba da masana da masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na jihar. Ya ce, “Mun ziyarci dukkanin wuraren tarihi da suke bayyana tarihin Masarautar Katsina da Daura. Mun samu shawarwari masu amfani daga masana, da kuma ra’ayoyin jama’a kan yadda za a farfaɗo da al’adunmu, musamman yadda za a inganta bukukuwan hawan sallah a masarautu.”
Ya ƙara da cewa, “Kwamitin ya buɗe ƙofa ga kowa wajen bayar da gudunmawa, kuma cikin ikon Allah, mun samu sakamako mai amfani wanda muka tattara cikin wannan rahoto. Muna fatan Gwamnatin Katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Umaru Radda za ta aiwatar da shawarwarin domin ci gaba da raya tarihi da al’adun jihar Katsina.”
Sanata Ida ya kuma yi godiya a madadin mambobin kwamitin ga gwamnatin jihar bisa damar da ta basu, tare da fatan alheri ga gwamnatin da al’ummar jihar gaba ɗaya.
A nasa jawabin yayin karɓar rahoton, Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Abdullahi Garba Faskari, ya yaba da yadda kwamitin ya gudanar da aikin da aka dora musu, yana mai cewa rahoton zai taimaka wa gwamnatin wajen tsara matakan ci gaba. “Gwamna Dikko Radda zai karɓi wannan rahoto hannu biyu, kuma za mu ci gaba da aiki akai don tabbatar da cewa tarihi da al’adun jihar Katsina sun ci gaba da samun kulawa da bunkasa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa don aiwatar da shawarwarin rahoton, tare da tabbatar da cewa abubuwan tarihi da al’adun gargajiya sun ci gaba da kasancewa a matsayin wani ginshiƙi na al’ummar jihar.