Sirajo Yazid Abukur Na Neman Masu Haka Kabarin Buhari Yayi Musu Kyauta

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes17072025_165428_Screenshot_20250717-175308.jpg


Biyo bayan faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, na wani mazaunin garin Daura, Muhammad Ali, wanda ya jagoranci wadanda suka haka kabarin marigayi tsohon shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, masoyan Buhari sun fara mayar da biki.

A halin yanzu dai, tuni shugaban Hukumar Kula da Gyaran Hanyoyi ta Jihar Katsina (KASSROMA), Engr. Sirajo Yazid Abukur, ya bada cigiyar wannan bawan Allahn, da alkawari ba shi kyautar Naira miliyon daya su raba, shi da mataimakansa.

Ya ce mataimakan Muhammad Ali, su biyu, kowannensu zai dauki Naira dubu dari biyu da hamsin domin su ja jari.

Shugaban na KASSROMA ya yaba wa gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, bisa irin damuwar da ya nuna da tabbatar da cewa an birne tsohon shugaban kasar cikin mutunci.

Ya ce Gwamna Radda ya shiga cikin hidimar dumu-dumu tun daga dauko gawar tsohon shugaban kasar har zuwa kai ta Daura, har zuwa yi mata sutura .

Abukur ya ce abin da ya fi burge shi shine yadda gwamnan ya cire babbar rigarsa ya shiga cikin masu aikin birne tsohon shugaban kasar, ya ce hakan ya nuna amanarsa da tawalu'u da kuma dabi'u na jagoranci.

Follow Us