ILIMIN ’YA’YA MATA: Gwamnan Zamfara Ya Tallafa Wa Yara Mata 8,225 Na Sakandare

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes17072025_164501_IMG-20250717-WA0179.jpg

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya raba tallafin kuɗi ga yara mata 8,225 a dukkanin ƙananan hukumomi 14 na jihar.

A ranar Larabar da ta gabata ne gwamnan ya fara rabon kuɗaɗe na ayyukan ACRESAL da Agile a ɗakin taro na Garba Nadama da ke sakatariyar J.B Yakubu a Gusau.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa an zabo ‘yan matan sakandaren 8,225 ne daga gidajen masu ƙaramin ƙarfi da marasa galihu.

Sanarwar ta ƙara da cewa, kowace yarinya za ta karbi tallafin Naira 40,000 don ci gaba da yi musu rajista da shiga makaranta.

“Ƙarin Naira dubu goma-goma da za a bayar na zangon karatu na biyu da na uku zai kawo adadin tallafin zuwa Naira 60,000 ga kowace ɗaliba wanda za a bayar ta bangaren iyaye ko masu kula da su, an amince da Naira Miliyan Ɗari Uku da Ashirin da Biyu ga wannan Kashi na Farko, a halin yanzu ana ci gaba da shirye-shiryen kashi na biyu ga masu cin gajiyar shirin.

A wajen bikin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa, taron a alamance yana bayar da tallafin kuɗi ne ga waɗanda suka ci gajiyar ayyukan ACReSAL da AGILE, waɗanda suka yi daidai da yadda gwamnatinsa ta mayar da hankali kan ilimi, ci gaba, da kare al’umma, da kuma kare muhalli.

Ya ce: “A ƙarƙashin wannan shiri na ACRESAL, mun bayar da tallafin ne ta Asusun Tallafawa Al’umma ga mutum 500 da suka amfana a Gusau, Bungudu, da Kaura Namoda da nufin tallafa wa ayyukan da suka shafi muhalli da tattalin arziki, wanda hakan ke nuni da ƙudurinmu na yaƙi da gurbacewar ƙasa, da inganta noma da inganta rayuwar al’umma a cikin matsalolin da ake fuskanta.

“Al’ummar mu na fuskantar wahalhalu kamar fafutukar mata wajen gina ƙananan sana’o’i, matasa masu neman tallafi. Asusun Tallafawa Al’umma yana ba da tallafi mai ɗorewa don tallafawa ci gaba, wanda ke nuna alamar juriya da riƙon amana. Ina kira ga masu cin gajiyar da su yi amfani da wannan tallafin cikin hikima da gaskiya, tare da tabbatar da sakamako na aminci a bayyane, sakamako mai kyau.

"Za a ta ci gaba da bayar da tallafin a cikin al'ummomi, ta hanyar amfani da mutane da yawa a tsawon lokaci. Ta hanyar amfani da shi yadda ya kamata, wannan shirin zai ba da misali na hada-hadar kuɗi da ɗorewar tattalin arziki."

Gwamnan ya ci gaba da cewa har yanzu ilimi shi ne babban fifikon gwamnatin sa.

“Mun himmatu wajen ganin mun magance tare da shawo kan duk wani shingen da ya shafi tattalin arziki, ababen more rayuwa, ko zamantakewa, waɗanda ke hana ‘ya’yanmu mata samun damar karatu da kuma kammala karatunsu, domin idan ka ilimantar da ’ya mace ko ka karantar da ƙauye ne, domin waɗannan ‘yan mata masu ilimi su na girma zuwa mata masu ƙarfin gwiwa, waɗanda suke ɗaukaka iyalansu, ƙarfafa al’umma, da kuma kawo ci gaba a jiharmu.

“Ina yaba wa dukkanin ƙungiyoyin da suka aiwatar da aikin a ƙarƙashin Ma’aikatar Muhalli da Albarkatun Masa da Ma’aikatar Ilimi, Kimiyya da Fasaha, da kuma abokan aikinmu na fasaha, saboda sadaukarwa da haɗin gwiwarsu wajen aiwatar da waɗannan muhimman shirye-shirye.

“Bari na tabbatar wa mutanen jihar Zamfara cewa wannan gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da manufofi da tsare-tsare masu ma’ana, musamman tun daga tushe, muna ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da gaskiya da kuma yi wa jama’armu hidima.

"Ga waɗanda suka ci gajiyar waɗannan tsare-tsare, ku tuna cewa abin da ku ke karba a yau iri ne. Ina roƙon ku da ku raya shi, ku shuka shi, kuma ku bar shi ya zama bishiyar canji ga iyalanku da al'ummominku."

Follow Us