Za a Yi Jana’izar Buhari a Daura Ranar Talata – Inji Gwamna Radda

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes14072025_115743_FB_IMG_1752492193896.jpg

Zaharaddeen Ishaq Abubakar | KatsinaTimes 

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya sanar da cewa za a yi jana’izar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Talata, 15 ga Yuli, 2025, a garinsu na Daura.

Da yake zantawa da manema labarai a Katsina ranar Litinin, Gwamna Radda ya bayyana cewa za a kawo gawar marigayin Buhari zuwa Katsina da misalin karfe 12:00 na rana, sannan a yi jana’izarsa da misalin karfe 2:00 na rana kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Ya ce an tsara jadawalin ne bayan tuntubar iyalan Buhari da kuma abokansa na kusa da shi a London, inda ya rasu a asibiti ranar Lahadi.

Gwamnan ya mika sakon ta’aziyya a madadin gwamnatin da al’ummar Jihar Katsina ga iyalan Buhari da daukacin al’ummar Najeriya, yana mai bayyana marigayin a matsayin gwarzon kasa da za a ci gaba da tunawa da ayyukansa har tsawon lokaci.

“Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya gafarta masa, ya ba shi Aljannatul Firdaus,” in ji Radda. “Haka kuma muna jajantawa mai girma shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa rasuwar wanda ya gada. Allah ya ba mu juriyar wannan babban rashi.”

Ya kara da cewa gwamnatin jihar Katsina tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya da iyalan marigayin, na ci gaba da shirye-shiryen gudanar da jana’iza mai kima da girma ga tsohon shugaban kasar.

Follow Us