KUNGIYAR POLO TA JIHAR KATSINA TA MIKA TA'AZIYYAR RASUWAR TSOHON SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes14072025_085742_IMG-20250714-WA0019.jpg



Inna lillahi wa inna ilayhi raji'un!

Kungiyar Wasan Polo ta jihar Katsina tana mai bayyana alhininta bisa rasuwar uban kungiyar kuma tsohon shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari.

Tsohon shugaban kasar ya kasance gwarzo wanda ya bayyana kishin kasa a matsayin shugaban mulkin soja da na farar hula.

Halayensa na gaskiya da gudun duniya abu ne mai wahalar samu a cikin shuwagabanni, kuma hatta abokan hamayyarsa sun shaida wadannan halayen, kuma za a cigaba da tunawa da shi a tarihin kasar nan.

Kungiyar Polo ta jihar Katsina tana mika ta'aziyyarta ga iyalansa, da mai girma Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, da masu martaba Sarakunan Katsina da Daura bisa wannan babban rashin.

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa Ya biya shi da Gidan Alhannar Firdausi kuma Ya ba iyalansa hakurin jure rashinsa.

Sa hannu:
Alh. Muhammadu Usman Sarki,
Shugaban Kungiyar Polo ta jihar Katsina

Follow Us