Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times
Wani Basarake a karkashin Masarautar Daura, Iliya Mantau, (Dagachin Mantau) wanda shi ne mai rikon sarautar garin Yan Maulu a ƙaramar hukumar Baure, Jihar Katsina, yana fuskantar zargin hannu dumu-dumu a cikin garkuwa da wata matar aure tare da ɗanta ɗan wata uku da kuma yi mata fyade duk da an biya kuɗin fansa har Naira miliyan 20.
Rahotanni sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne kusan shekara guda da ta gabata, inda wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka sace Zulaihatu Sidi da jaririnta. Bayan mako guda da sace su, an sake su bayan an biya kuɗin fansa, amma duk da haka sai da aka yi wa matar fyade.
Wannan lamari ya tayar da kura a garin Yanmaulu dake ƙarƙashin Masarautar Daura, inda matasa suka fito zanga-zanga domin neman a tabbatar da adalci ga Zulaihatu da yaronta.
Jagoran zanga-zangar, Muhammad Abdullahi, ya shaida wa manema labarai cewa, “A yanzu shekara ɗaya kenan da Zulaihatu da ɗanta suka shiga hannun masu garkuwa. Koda aka biya kuɗin fansa, sai da aka ci zarafinta ta hanyar fyade. Muna da tabbacin cewa akwai wasu jiga-jigan mutanen da ke da hannu cikin wannan aika-aika, ciki har da Dagachin garin mu na Mantau Ilya mai rikon sarautar garin 'Yan Maulu.”
Muhammad ya ƙara da cewa, mutane takwas ne aka kama da hannu a lamarin, kuma yawancinsu daga ƙauyen Mantau ne. Ya ce daga cikin waɗanda ake zargi akwai Iliya Mantau, wanda ke matsayin wakilin Hakimin Yanmaulu kuma wanda ake zargin ya shugabanci masu garkuwa da mutane a yankin.
Sai dai, masu zanga-zangar sun bayyana damuwa da cewa, duk da an gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu, Masarautar Daura na ƙoƙarin ganin an saki Dagachin da ake zargi, lamarin da ya tayar musu da hankali.
“A saboda haka muka fito domin mu bayyana damuwarmu game da yunkurin da Masarautar Daura ke yi na shawo kan shari’ar domin a saki Dagachin,” in ji Muhammad.
Sun yi kira ga Gwamna Dikko Umar Radda da ya shiga cikin lamarin kai tsaye domin tabbatar da an yi wa Zulaihatu da ɗanta adalci, tare da gurfanar da duk masu hannu a gaban shari’a ba tare da wata rufa-rufa ba.
Har zuwa yanzu, babu wata sanarwa daga Masarautar Daura dangane da zargin da ake yi wa Iliya Mantau, wanda ke tsare tare da wasu da ake zargi da hannu a garkuwa da mutane da cin zarafin mata.
A cewar wasu daga cikin mazauna garin Mantau, har yanzu babu wata takarda daga hukumomi da ke nuna cewa an dakatar da mai garin daga mukaminsa, duk da cewa jami’an tsaro sun gudanar da bincike kuma sun tsare shi tare da sauran mutane da ake zargi.
Mazauna yankin da masu fafutukar adalci sun ce dole ne a cire siyasa da shisshigi daga wannan lamari domin ganin gaskiya ta samu nasara, musamman ganin cewa lamarin ya shafi basarake a wani babban yanki na masarauta.