Gwamnatin Jihar Katsina ta bai wa kowanne daga cikin mahajjatanta 2,047 da ke sauke farali a bana kyautar Riyal 300 domin sauƙaƙa musu gudanar da ibadunsu a ƙasa mai tsarki.
Haka kuma, gwamnati ta biya kuɗin Hadaya na Riyal 600 ga kowanne mahajjaci domin cika sharuddan aikin Hajji yadda ya kamata.
Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina kuma Amirul Hajj na bana, Malam Faruk Lawal Jobe ne ya sanar da hakan a yayin ziyarar duba yanayi da jin ƙorafin mahajjata a sansanonin Arafat.
Ya isar da saƙon gaisuwa da fatan alheri daga Gwamna Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, wanda ya nuna jin daɗinsa kan yadda mahajjatan ke gudanar da kansu cikin tsari da kwanciyar hankali. Ya kuma bukaci su ci gaba da kasancewa cikin natsuwa da addu’o’i.
Malam Faruk Lawal Jobe ya yaba da irin shirin da jami’an aikin Hajji suka yi musamman a fannin abinci da masauki a sansanonin Mina da Arafat.
Wasu daga cikin mahajjatan da suka tofa albarkacin bakinsu sun nuna godiyarsu ga Gwamna Dikko Radda bisa wannan kyauta da tallafi. Sun kuma jaddada niyyarsu ta ci gaba da yi masa addu’a domin samun nasara a kokarinsa na gina Jihar Katsina.