Gwamnatin jihar Katsina, ta bayyana makasudin ziyarar kwanaki biyu da shugaban kasar Nijeriya, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu zai kawo a jihar a ranar juma'ar nan 2 ga Mayu 2025.
Kwamishina na labaru na jihar, Dr. Bala Salisu Zango ne ya zayyana dalilan a wani taron manema labarai kan zuwan shugaban kasar da aka gudanar gidan gwamnatin jihar a ranar Larabar nan, wanda jaridun katsina times suka shaida.
Dr. Bala ya ce, dalilin ziyarar shugaban kasar shi ne domin kaddamar da wasu ayyuka wanda gwamnatin jihar karkashin shugabancin Dr. Umar Radda ta gabatar a cikin shekaru biyu na mulkin jihar.
"Cikin shekaru biyu gwamnatin jihar katsina karkashin jagorancin Dr. Malam Dikko Umaru Radda Ph.d ta aiwatar da ayyuka wadanda suka inganta rayuwar al'ummar jihar katsina, kama daga abin da ya shafi kiwon lafiya, harkar noma da sauran harkoki na rayuwar dan'adam wadanda suka kawo ci gaba a jihar." In ji shi
Adon haka, Dr. Zango ya ce shugaban kasa zai kawo ziyarar kaddamar da wasu daga cikin muhimman ayyukan da gwamnatin ta gabatar, inda ya bayyana cewar shugaban zai kaddamar da biyu daga cikin muhimmansu.
"A wannan ziyarar zai kaddamar da biyu daga cikin manya-manyan ayyuka da wannan gwamnati ta aiwatar, wanda lokaci ba zai ba da damar ya kaddamar da dukkan ayyukan ba."
Ya ci gaba da cewar, "Daya daga ciki shi ne hanya ta ratse wadda ke kaucewa cunkuso (Bypass), wadda ta tashi daga hanyar Dutsin-ma ta hade da hanyar Kano, ta zagaya ta ratsa hanyar Daura ta tafi ta hade da hanyar zuwa 'Yandaki da ke kan hanyar zuwa Kaita."
Ya ce, sanin kowa ne cewar hanyoyi suna da muhimmanci wajen bunkasa harkokin arziki na al'umma, domin ana samun sauki wajen tafiye-tafiye na kasuwanci.
"Hanyoyi suna daya daga cikin ayyukan da wannan gwamnati ta wa muhimmanci domin saukakawa al'ummar jihar katsina da ma wadanda suka zo harkar kasuwanci a jihar, wanda wannan zai kawo wa jihar ci gaba da bunkasar kasuwanci a jihar." Ya bayyana hakan a matsayin dalilin saka su a ciki ayyukan da shugaban kasar zai kaddamar.
Abu na biyu da shugaban zai kaddamar, Dr. Zango ya bayyana cibiyar da aka tanada don hada kayan aikin gona na zamani a matsayin daya daga ciki.
"Bayan haka wani babban kasuwanci da shugaban kasa zai kaddamar shi ne "Agric Mechanization centre" cibiyar da aka tanadi kayan aikin gona na zamani wanda ake amfani da Mashina da injina wajen harkar noma, wadda za a debi matasan jihar katsina a koya masu yadda ake halhada su."
Daga karshe, Dr. Zango ya bayyana ziyarar a matsayin wadda za ta kawo wa alummar jihar Katsina ci gaba kwarai da gaske, domin za a samu a samu tattauna wasu batutuwa da suka shafi jihar musamman harkar tsaro, inda masu ruwa da tsaki a harkar za su tattauna kan lamarin, tare da kuma sauran wasu abubuwan ci gaba da dama.