Na Karɓi Mulki Lokacin Da Jihar Zamfara Ke Fama Da Matsaloli Ta Kowace Fuska– Gwamna Lawal

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes14042025_170910_IMG-20250414-WA0009.jpg



Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya bayyana cewa, lokacin da ya karɓi mulki daga tsohon gwamna Bello Matawalle, jihar Zamfara tana cikin matsaloli ta kowace fuska.

Ya bayyana cewa rashin tsaro ya yi katutu, tsarin ilimi ya rushe, ɓangaren kiwon lafiya mara kyau, da kuma ɗumbin basussuka da aka biyo jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da tashar Arise TV a ranar Litinin ɗin nan.

Ya ce, “Lokacin da na karɓi mulki a matsayin gwamna, jihar Zamfara tana cikin wani yanayi mai matuƙar muni a kowanne ɓangare na rayuwa, matsalar tsaro ta kai ƙololuwa, ilmi ya yi ƙasa warwas, kiwon lafiya ya taɓarɓare ta yadda ba za a iya misaltawa ba."

“Babu ko ɗigon ruwa guda a jihar Zamfara na tsawon watanni biyar kafin na hau mulki, amma mun samu damar warware wannan matsala cikin kwana uku kacal."

"Gaskiya bashin da aka bari ba kaɗan ba ne, amma a matsayin shugaba, dole ne na nemo mafita domin gyara lamarin," inji Gwamna Lawal.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa ya gaji ɗumbin basussuka daga wajen tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle, inda ya ce Naira Miliyan Huɗu kacal aka bari a Baitulmalin jihar a lokacin da ya karɓi mulki.

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana irin basussukan kuɗi da ya gada lokacin da ya hau mulki, da kuma yadda ya biya albashin ma’aikata da fansho da sauran basussuka.

"Lokacin da na hau mulki, ba komai a cikin Baitulmali na jihar. Na gaji bashi mai yawa, Naira miliyan huɗu ne kacal na tarar."

"Dukkan bayanan suna nan, bashin albashin ma’aikata na tsawon watanni huɗu da rabi, bashin ɓangaren shari’a na Naira Biliyan 1.6, WAEC Naira Biliyan 1.6, NECO Naira Biliyan 1.4, da sauran ƙalubale masu yawa."

"Abu na farko da na fara yi shi ne biyan bashin albashi. Na nemi yarjejeniya da WAEC da NECO domin ’ya’yan mu su samu su rubuta jarrabawa, kuma ba kawai jarrabawar ba, har da samun shaidar kammala karatu da suka rubuta a baya amma suka kasa karɓa saboda rashin biyan kuɗi."

"Lokacin da na hau mulki, albashin ma’aikacin gwamnati a jihar Zamfara N7,000 ne kacal a matakin jiha da Ƙananan Hukomomi. Dole ne na gaggauta ƙara shi zuwa mafi ƙarancin albashi na N30,000.”

“Ba haka kawai ba, tun daga shekarar 2011, ba a biyan tsofaffin ma’aikata fanshonsu ba, har bashin ya kai Naira Biliyan 16.5, wanda Alhamdulillah na samu na biya su baki ɗaya a watan da ya gabata."

"Duk wani ma’aikaci daga 2011, an biya masa fansho, kuma yanzu muna biyan albashi mafi ƙaranci na N70,000," inji Gwamna Dauda Lawal.

Follow Us