Muhammad Ali Hafizy, Katsina Times.
A ranar Asabar 08 ga watan Maris 2025, Majalissar Matasa ta kasa reshin Jihar Katsina ta gudanar da zaben sabbin shuwagannin Majalissar a matakin jiha, wanda ya gudana a filin wasanni na Muhammadu Dikko Stadium dake cikin birnin Katsina.
Mai ba gwamnan Jihar Katsina shawara akan harkokin Matasa, Hon, Abubakar Tsanni, a lokacin da yake gudanar da jawanin maraba da Matasan, ya nuna jij dadin shi wajen bayar da hadin kai da suka yi na kaucema duk wani rikici da ya so ya afko, tare da bayar da shawarwarin ga Matasan domin ganin an gudanar da zaben lafiya ba tare da wata mastsala ba.
An gudanar da zaben lafiya kuma an kammala lafiya ba tare da wata mastsala ba, mutane sun kada kuri'un su da dukkannin yan takarkaru da suke ganin zasu yi masu abinda ya dace, da kuma kawo cigaba a cikin rayuwar su.
Daga karshe Comrd Yusuf Abubakar Papa ya Lashe zaben Shugabancin Majalissar da kuri'u kimanin 978, tare da mataimakiyar shi Amb Khadija Suleman Saulawa.