Masana Sun Bukaci Sauya Tsarin Tsaro a Arewa Maso Yamma, Tsohon

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes23022025_070543_Screenshot_20250223-080330.jpg

Minista Ya Jaddada Bukatar Gaskiya a Shugabanci

Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times 

Tsohon Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojan Ƙasa, Manjo Janar Sani Kukasheka Usman (ritaya), ya bukaci a sake fasalin dabarun tsaro a yankin Arewa maso Yamma domin magance matsalolin tsaro da suka addabi yankin.

Janar Kukasheka ya bayyana haka ne a taron kwanaki biyu da aka shirya wa jami’an gwamnati da masana tsaro na Jihar Katsina a Kaduna, wanda Gwamnatin Katsina ta shirya. Ya jaddada cewa dole ne a wuce tunanin dogaro da matakan tsaro na gargajiya.

A cewarsa, “Jihar Katsina, kamar sauran jihohin Arewa maso Yamma, na fama da matsalolin tsaro irin su ta’addanci, garkuwa da mutane da rikicin manoma da makiyaya, wanda ke barazana ga gwamnati, ci gaban tattalin arziƙi da zaman lafiya. Dole ne a haɗa matakan tsaro, dabarun zaman lafiya da hanyoyin magance rikice-rikice don shawo kan wadannan matsaloli.”

Ya yaba da sabbin matakan tsaro da gwamnatin Gwamna Dikko Umaru Radda ta ɗauka, kamar ƙirƙirar rundunar tsaro ta al’umma da kuma kafa ma’aikatar tsaro ta musamman, amma ya ce dole ne a zurfafa dabarun tsaro. “Ba wai a dogara da ‘yan sanda kaɗai ba. Dole ne a ƙirƙiri shirye-shiryen tattalin arziƙi da za su bai wa matasa damarmaki na halas. Dole ne shugabannin gargajiya da na addini su shiga tattaunawa. Haka kuma, dole ne mu inganta tattara bayanan sirri domin mu kasance gaba da barazanar tsaro,” in ji shi.

Ya bayyana cewa tsaro ba wai yana nufin amfani da makamai kaɗai ba, yana buƙatar nagartaccen shugabanci, samar da dama ga al’umma da haɗin kai. “Tsaro ba wai kawai makamai da jami’an tsaro ba ne. Nagartaccen shugabanci ne, samar da fata da damarmaki ga mutane, da kuma haɗa kan kowa don samo mafita mai dorewa,” in ji shi.

A wani zama na taron, tsohon Ministan Yaɗa Labarai, Frank Nweke II, ya bukaci shugabannin Jihar Katsina da su rungumi shugabanci na gaskiya da kuma sauya tunanin jagoranci. “Duk wani shugabanci da bai inganta rayuwar al’umma ba, ba shugabanci ba ne, zama kan kujera kawai ake yi,” in ji shi.

Ya ambato marigayiya Dr. Dora Akunyili a matsayin misalin jagora mai gaskiya, wanda ta canza Hukumar NAFDAC daga gurbatacciyar hukuma zuwa wadda aka mutunta saboda yaƙi da jabun magunguna. Ya bukaci shugabannin Katsina su fifita buƙatun al’umma a kan komai. “Dr. Akunyili ba wai kawai ta jagoranci NAFDAC ba ne—ta sauya tsarin sa gaba ɗaya. Ta kori jami’ai masu cin hanci, ta ƙarfafa dokoki, ta ƙirƙiri haɗin gwiwa, kuma ta tabbatar da cewa ana iya samun sauyi idan shugabanni suka sanya al’umma a gaba,” in ji shi.

Dangane da matsalolin da suka addabi Katsina, Nweke ya ce cin hanci, kin sauya hanyoyin aiki da rashin kuzari na daga cikin manyan matsalolin da ke hana cigaba. A cewarsa, “Wadannan matsaloli ba kawai kalmomi ba ne, sune tubalan da ke hana yara samun ingantaccen ilimi, iyalai samun lafiyar kirki, da al’ummomi samun tsaro.”

Ya gabatar da shirin matakai biyar da suka haɗa da yanke shawara bisa gaskiya, jagoranci da misali, ƙarfafa ma’aikata ta hanyar horo, amfani da bayanai wajen yanke hukunci da kuma kawar da shingayen aiki tsakanin ma’aikatu.

Taron kwanaki biyu da aka fara daga ranar Alhamis, 20 ga Fabrairu zuwa Juma’a, 21 ga Fabrairu, 2025, an shirya shi ne domin bai wa manyan jami’an Gwamnatin Katsina dabarun magance manyan matsalolin da ke fuskantar jihar.

Follow Us