Daga Sulaiman Umar
KATSINA – Ofishin Mai Binciken Kudi (Auditor General) na Jihar Katsina ya gudanar da gagarumin taron ban kwana domin karrama wasu daga cikin ma’aikatanta da suka yi ritaya. Taron ya gudana a yau Alhamis, tare da halartar manyan jami’an ofishin da sauran ma’aikatan ma’aikatar.
Shugaban Ma’aikatar Odita General, Shuaibu Aliyu, wanda ya jagoranci taron, ya bayyana cewa ma’aikatan da suka yi ritaya sun bayar da muhimmiyar gudunmawa ga ma’aikatar, inda suka kasance ginshikai wajen tabbatar da ingantaccen aiki da da’a a fannin binciken kudi na jihar. Ya bayyana godiya ga masu ritaya bisa irin namijin kokarinsu da sadaukarwarsu na tsawon shekaru da suka kwashe suna hidimtawa jihar.
Baya ga haka, hukumar ta karrama su da lambobin yabo domin nuna godiya da yabawa ga irin gagarumin kokarin da suka yi wajen gudanar da ayyukansu da kuma koyar da sabbin ma’aikata da suka shigo bayan su. Wannan karramawa, a cewar shugaban ma’aikatar, zai zama abin koyi ga ma’aikatan da ke ci gaba da aiki domin kara himma da jajircewa.
A yayin bikin, wasu daga cikin ma’aikatan da suka yi ritaya, ciki har da Musa Yakubu, Muhammadu Abdu, Malam Bishir, Sani Abdu, da kuma Sani Tukur, sun bayyana jin dadinsu da irin karamcin da ma’aikatar ta nuna musu. Sun gode wa abokan aikinsu da shugabanni bisa goyon bayan da suka basu a lokacin da suke aiki. Haka kuma sun yi amfani da damar wajen yi wa dukkan ma’aikatan fatan alkhairi tare da neman yafiya, ganin cewa sun kwashe shekaru 35 suna aiki tare a ma’aikatar.
Taron ya kasance cike da kewa da jin dadi, yayin da abokan aiki suka yi musayar fatan alkhairi da juna, tare da bukatar ci gaba da irin wannan karramawa domin kara inganta jin dadin ma’aikata masu ritaya a jihar.