MUTUM DUBU DARI BIYAR NA NEMAN AIKIN KWASTAM NA MUTANE DUBU HUDU KACAL A NIJERIYA

top-news


Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta bayyana cewa ta karɓi Takardun neman Aiki har guda 573,519 a cikin shirin ɗaukar ma’aikata na shekarar 2024/2025 da aka gudanar ta hanyar shafinta na yanar gizo.  

A baya-bayan nan, Ministan Kuɗi, Mista Olawale Edun, ya tabbatar da amincewa da ɗaukar sabbin ma’aikata 3,927 a hukumar Kwastam ta Najeriya. Wannan na nufin cewa daga cikin takardun neman aiki 573,519, hukumar za ta ɗauki ma’aikata 3,927 kacal da suka cancanta.  

Kakakin Hukumar Kwastam na Ƙasa, Abdullahi Maiwada, ya yi karin bayani  a wata tattaunawa, inda ya ce an samu waɗanda suka nema daga matakai daban-daban, ciki har da masu shaidar digiri na Jami’a, HND, da kuma masu takardar sakandare.  

Da yake bayani, Maiwada ya ce:  
“Na so bayyana yawan waɗanda suka nema. Muna da rukunai biyu na ma’aikata – akwai ma’aikatan da suka ƙware (support staff) sannan akwai ma’aikatan ayyukan yau da kullum (general duty).  

“Don aikin yau da kullum (general duty) a ƙarƙashin matakin Supretendent, an samu takardun neman aikin daga mutane 249,218.  

“Na Supretendent a matsayin ma’aikatan ƙwararru (support staff) an samu kakaradu 27,722 daga masu shaidar HND da digiri na Jami’a.  

“Don matakin Inspector, waɗanda ake tsammanin su kasance da shaidar NCE ko ND, mun samu takardu 115,634 don ayyukan yau da kullum, yayin da masu ƙwarewa (support staff) suka kasance 12,952.

“Game da matakin Customs Assistants, waɗanda ake buƙatar takardar sakandare, akwai rukunai biyu: waɗanda ke da sakamakon jarabawa mai ƙididdigar ‘credit’ biyar (tare da lissafi da Ingilishi), da waɗanda ba su da su. Don aikin yau da kullum, mun samu aikace-aikace daga mutane 153,593, yayin da masu ƙwarewa (support staff) suka kasance 14,400.”