Yadda Naira Biliyan 1 Ga Kowanne Dan Majalisa Ta Hana Su Yiwa Tinubu E-HO a Lokacin Gabatar da Kasafin Kudi

top-news

Katsina Times 

A wata yarjejeniya don kwantar da hankulan 'yan Majalisar Wakilai game da kudirorin sake fasalin haraji, Shugaban kasa Bola Tinubu ya kara wa’adin kudin ayyukan mazabu zuwa Naira biliyan daya ga kowanne dan majalisa.  

A ranar Laraba, Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin kudin 2025 mai na Naira Tiriliyan 47.90, tare da tabbatar wa jama’a cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da karfafa tattalin arzikin kasar ta hanyar shirye-shiryen inganta tattalin arziki, kashe kudaden gwamnati da kuma kashe kudade ba tare da haifar da hauhawar farashi ba.  

A baya dai, 'yan majalisar sun kammala shirye-shiryen rera kalaman “a’a  bamu yadda ba, ga kudirorin harajin” da “janye kudirorin haraji” a lokacin da shugaban zai gabatar da kasafin kudin 2025 a yayin haduwar majalisun tarayya ta Sanatoci da ta Wakilai.  

Sai dai, bayan da fadar shugaban kasa da shugabannin majalisar suka gano wannan shirin na 'yan majalisar, majalisar ta shirya taron gaggawa na kulle kofa tare da dukkan 'yan majalisar da safiyar ranar Laraba.  

“An gama shiryawa don rera ‘a’a bama yi, ga kudirorin haraji’ a lokacin jawabin Shugaba Tinubu, amma da aka gayyaci 'yan majalisar zuwa wani taron boye da shugabannin majalisar da misalin karfe 9:30 na safe a ranar Laraba,” inji wata majiya da ta san yadda taron ya gudana.  

“A yayin taron, sun yi kira ga 'yan majalisar da su mutunta zauren majalisa da kuma kyakkyawar dangantaka da bangaren zartarwa, su soke shirinsu na yiwa shugaban ƙasa Eho don zai tayar da abin kunya kuma zai tada hankalin shugaban kasa.

“Daga nan suka sanar da cewa shugaban kasa ya karfafa kudin ayyukan mazabu zuwa Naira biliyan daya ga kowanne dan majalisa.”  

Duk da cewa za a sanya kudin a kasafin kudin 2025 da sunan ayyukan mazabu, kwararrun harkokin majalisa sun bayyana cewa wannan faɗa ce kawai, domin za a bai wa kamfanonin da 'yan majalisar suka zaba kwangilar ayyukan.  

Jaridar Daily Nigeria ba ta iya tabbatar da irin abin da sanatoci suka samu ba, amma wasu majiyoyi sun ce yana tsakanin Naira biliyan biyu zuwa biliyan hudu ga kowanne sanata.  

A cikin kasafin kudin 2024, 'yan majalisar sun samu daga Naira miliyan 200 zuwa miliyan 500, ya danganta da irin kusancinsu ga Kakakin Majalisar Wakilai, Abba Tajudeen, ko Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi, Abubakar Bichi.  

A watan Yuli, kowanne sanata da dan majalisa sun samu Naira miliyan 500 da miliyan 200 bi da bi bayan amincewa da bukatar shugaban kasa na kara kasafin kudin 2024 da Naira tiriliyan 6.2.  

A cewar majiyoyin majalisa, kudaden da aka bayar a watan Yulin an sanya su a wasu hukumomi karkashin ma’aikatu na Noma da Albarkatun Ruwa.  

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun majalisar wakilai, Akin Rotimi, bai mayar da martani kan tambayoyin wakilinmu ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.