KIWON LAFIYA: CUTAR CIWON SANYIN MATA (GONORRHOEA)
- Katsina City News
- 04 Dec, 2024
- 19
Wannan cuta ce da wasu kwayoyin cuta ke haddasawa, kuma ta fi kamari a jikin mata fiye da maza saboda tsarin al'aurarsu.
26.1 Alamomin Cutar
Alamomin cutar suna bayyana bayan kwanaki bakwai zuwa goma da kamuwa da ita. Su ne:
1. A wajen namiji:
- Kumburi a mafitsara.
- Jin ciwo yayin fitsari.
- Zubar wani ruwa mai kauri daga al’aura.
2. A wajen mace:
- Kumburi a bakin mahaifa.
- Zubar wani ruwa mai wari da kalarsa ta zama kore.
- Jin ciwo mai tsanani a mara.
- Kumburi a hannuwan mahaifa (fallopian tubes).
3. A wasu lokuta, cutar na haddasa rashin haihuwa saboda illa ga tsarin haihuwa.
4. Idan mace mai ciki ta kamu, cutar na iya shafar jaririnta, musamman idan jaririn ya kamu da ciwon idanu wanda zai iya kai ga makanta.
Yadda Ake Gane Cutar
A asibiti ne kawai ake iya tabbatar da cutar ta hanyar gwaje-gwaje. Saboda haka, idan an ga wadannan alamomi, ya kamata a gaggauta zuwa asibiti domin neman magani.
Yadda Ake Kare Kai
Domin kaucewa wannan cuta:
- A nisanci aikata zinace-zinace.
- A gaggauta neman magani idan an fara ganin alamomi.
Shawara:
Cutar cizon bera da ciwon sanyin mata na daga cikin cututtuka masu illa ga rayuwar dan Adam. Yana da matukar muhimmanci a rika kula da tsafta da nisantar dabi’u marasa kyau domin kare kai daga kamuwa da wadannan cututtuka.
Daga littafin Safiya Ya'u Yemal