Aminu Balele Kurfi Ya Samar da Fomfuna Masu Amfani da Hasken Rana a Mazabar Dutsin-Ma da Kurfi
- Katsina City News
- 04 Dec, 2024
- 24
A kokarinsa na tabbatar da wakilci mai inganci, Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Dutsin-Ma da Kurfi, Hon. Aminu Balele Dan'arewa, ya kaddamar da shirin samar da famfunan ruwa masu amfani da hasken rana domin magance matsalar karancin ruwa a wasu sassan mazabar.
An samar da famfunan a wasu yankuna na kananan hukumomin Dutsin-Ma da Kurfi, inda kowanne famfo ya lakume kimanin Naira miliyan 25.
Yankunan da Aka Kaddamar da Aikin sun hada da Dutsin-Ma: Garin Dabawa - Dabawa Ward, Sabon Garin Safana - Dutsin-Ma 'B', Wakaji - Dutsin-Ma 'A', Yarruma - Kutawa Ward, Shema Gari - Shema Ward, Garin Karofi - Karofi 'A' , Fagguwa - Karofi 'B', Garin Kuki - Kuki 'A'
Tsawa Tsawa - Kuki 'B'.
Sai Kurfi: Garin Kurfi - Kurfi 'A' Ward, Kurfi 'B' ,Kauyen Dandawa, Tauri 'B', Kaware 01, Birchi Ward, Tashar Barau, Wurma 'B', Kauyen Lambo, Barkiya Ward, Yarmarke 01, Rawayau 'A' ,Rawayau 'B', Kauyen Bura Brain, Dangawo
Dan Majalisar ya bayyana cewa an yi adalci wajen rarraba wadannan ayyuka, ba tare da la’akari da halin da aka bari wasu yankuna ba a baya. Wannan mataki ya kasance ne don tabbatar da samun ci gaba mai dorewa a dukkan sassan mazabar.