DUK MAI BUƘATA "TWO SIMS CE, FULL OPTIONS" ...Haɗuwa Ta Da Wata Fitsararra A Legas
- Katsina City News
- 24 Nov, 2024
- 209
@Ɗanjuma Katsina
Abubuwa da yawa masu ban al'ajabi sun same ni a wannan aikin namu na jarida daga cikin su akwai:-
A 1998 wani matashi ya same ni har ɗaki na, lokacin ina zaune a Kano, ya ce man in kalle shi. Ya ce to yana ɗauke da cutar ƙajamau, ko in ce kabari salamu alaikum (AIDS).
Dogon labari ne, amma na girgiza a lokacin.
A 2012 kuma, wani mutum ya kira ni a Zariya ya ce mu haɗu zai faɗa man wani sirri. Ya ce ya ɗau lambata ne a shafina na jaridar ALMIZAN mai suna HANTSI. Muka yi mahaɗa a wani otel da ke hanyar Kaduna. Ya faɗi man ɗakin da zan same shi.
Ina shiga, ba wani dogon Turanci sai ya ce, shi ne shugaban sashen siyasa na ƙungiyar Boko Haram a yankin Arewa.
Labari zai ban. In har na san ba zan iya buga shi a jarida ba, to kar a fara. Don ya faɗi man ko dai ya fito, ko in rabu da raina.
Na ce zan yi shawara. Ya ce in na amince in dawo, in ban amince ba, Allah raka taki gona.
Ban koma ba. Kuma gaskiya bai sake kira na ba.
Na uku, a 2003 ina binciken wata badaƙalla, sai wani mutum ya kira ni har ofis, bayan tabbatar man da abin da nake bincike, sai ya ce, matansa na aure huɗu, 'ya'yansa 20, jikokinsa bakwai, saura shekara ɗaya ya yi ritaya. Ya ɗauko Alƙur'ani ya yi rantsuwa sau uku. Ya ce, "Kai ka yi kaɗan ka ɓata wa wannan zuriya da na kafa suna, ka kashe ni da raina. Ko ka bar wannan labarin, ko kuma ni zan kashe ka kafin jaridar ta fito!"
Na huɗu, a wannan shekarar 2024, wata hidima ta kai mu Legas, muna zaune da abokan tafiya ta a bakin Swimming Pool na otel ɗin da na sauka, an kawo mana gasasshen kifi da lemu kala-kala da ruwa muna ci da sha a tsanake. Sai ga wata yarinya Bahausa cikakka da shigar Hausawa ta ce, mana ta zauna?
Ɗaya daga cikinmu ya ce, "Ai wuri na kowa ne." Ya amince mata don mu ji da wacce ta zo.
Sai kawai ta ce mana ita fa in har ana so, to ita
TWO SIMS ce, kuma FULL OPTION.
Bayanin ma'anar TWO SIMS, FULL OPTIONS da ta yi mana ya ta da mana hankali.
Daga cikinmu wani ya yi mata kyautar kuɗi. Wannan kuɗin sai ya jawo ta ɗauko wata wayarta mai 'password' kai ka ce Bankin Duniya ne a cikinta.
Da farko dai aka sa 'thumbprint', aka sa wasu lambobi, sannan aka yi wani rubutu, sannan aka yi murya, sai wayar ta buɗe.
A ciki ne muka ga wasu hotuna masu tada hankali. Haka na wangame baki cikin girgiza da mamaki ina kallon yarinyar nan.
Can aka kira ta a waya. Wannan shi ne rabuwarmu.
_Ɗanjuma Katsina, marubuci ne a jaridar ALMIZAN, kuma shi ne mawallafin jaridun Katsina Times da Mujallar Katsina City News._