Mayar da Kudin tsintuwa: An yi wa Bakano ruwan Naira Miliyan 250

top-news

Daga Salihu Makera da Idowu Isamotu da Sagir
Kano Saleh

Bakanon nan mai tuka Keke NAPEP ko A Daidaita Sahu mai suna Auwalu Salisu, wanda ya mayar da kudin tsintuwa har Naira miliyan
15 ga mai shi, kakarsa ta yanke saka, inda aka yi masa ruwan Naira miliyan 250 tare da daukar nauyin karatunsa har matakin digirin digirgir. 

Zuwa Kamfanin Jaridun Media LEADERSHIP Group ne ya karrama Auwalu da lambar yabo a matsayin Fitaccen Matashin Shekarar 2023" a ranar Talata a Abuja, sakamakon nuna gaskiya da rikon amana wajen mayar da Naira miliyan 15 ga wanda ya hau A Daidaita Sahunsa kuma ya mance da su. 

Daga farko dan takarar Shugaban Kasa na Jamiyyar LP a zaben 2023, Peter Obi da Mataimakinsa, Datti Baba- Ahmed ne suka bayyana daukar nauyin karatun Auwal Salisu.

 Peter Obi da Datti sun dauki nauyin Auwalu mai shekara 22 har sai ya kammala karatua Jamiar Baze mai zaman kanta da ke Abuja, inda za su rika biya masa kudin makaranta da na abinci da na dakin kwana da na sauran bukatu. Sai Gwamnan Jihar Neja Mohamammed Umar Bago, wanda aka karrama matsayin "Fitaccen Gwamnan Shekara 2023" ya bayyana bayar da tallafin karatu na Naira miliyan 250 ga Auwalu saboda nuna halin gaskiya, inda ya bukaci matasan Nijeriya su yi koyi da shi. 

Gwamna Bago ya ta ce, Auwalu zai samu tallafin karatu na Naira miliyan 50 daga gare shi, sai wata miliyan 50 daga Shugaba Bola Tinubu, sai ministocinsa Naira miliyan 50 sai gwamnonin APC Naira miliyan 50, sai kuma gwamnatin Jihar Neja Naira miliyan 50. Gwamna Umar Bago ya ce zai kuma sanya wa daya daga cikin titunan da yake ginawa a Neja sunan Bakanon mai tuka A Daidaita Sahu kuma dan wani mahauci. 

Da yake nuna jin dadi da godiyarsa kan lambar girmamawar, Auwalu ya celambar fitaccen matashi ta LEADERSHIP daya ce daga cikin karramawa da dama da ya samu tun lokacin da ya mayar da Naira miliyan 15 da ya tsinta a A Daidaita Sahunsa ga mai su dan kasar Chadi. "Ina yabo da godiya ga Jaridar LEADERSHIP kan wannan karramawa, Na yi matukar murna saboda ban tsammaci mayar da kudin ga mai su zai jawO min irin Wannan daukaka ba. "Duk da cewa yunwa ba za ta bar wasu mutane su mayar da kudin ba, amma akwai bukatar kafi karfin zuciyarka, saboda ta fi komai. 

Na samu kyaututtuka da lanmbobin yabo da daga mutane dama ciki har da 'yan Majalisar Jihar Kano Dokokin da Mai martaba Sarkin Kano, bayan na mayar da kudin ga mai su. Kuma wannan karramawa ta LEADERSHIP shaida cewa yana da kyau mutum ya ksance mai gaskiya," in ji Auwalu. 

Masu shirya taron bayar da lambobin yabo a taron Shekara-Shekara na LEADERSHIP sun ce a kasar da matasan yanzu da dama ba su dauki gaskiya muhimmanci da ba, Auwalu ya sake farfado da kyakkyawar fata ga manyan
gobe ta wajen nuna gaskiya da rikon amana.
Auwalu ya mayar da kudin da fasinjan ya bari a
cikin babur dìnsa ne bayan ya ji cigiyar kudin a gidan rediyo. Wani dan kasuwa dan
kasar Chadi da ya je Kano yin sayayya ne ya manta kudin a cikin babur din.

NNPC Advert