ZAMFARA ZATA GINA WAJEN TSAYAWAR MOTOCI
- Katsina City News
- 27 Feb, 2024
- 384
@ Katsina Times
Gwamna Dauda Lawal ya karɓi baƙuncin shugabannin Ƙungiyar Masu Motocin Haya ta Nijeriya, NARTO, da direbobin tankar mai (PTD), reshen Jihar Zamfara.
Taron da aka gudanar a ranar Talata a gidan gwamnati da ke Gusau, ya tattauna batutu wa da dama da suka haɗa da gina wuraren ajiyar ababen hawa da hallale matsalar cunkoson ababen hawa a babban birnin jihar Zamfara.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta bayyana cewa za a samar da wuraren ajiyar ababen hawa ne domin inganta zirga-zirgar ababen hawa tare da rage cunkoso a wani ɓangare na aikin sabunta birane.
Ya ƙara da cewa, Gwamna Lawal na shirin gina wuraren tsayawar motocin ne a manyan mashigan babban birnin jihar biyu domin inganta harkokin sufuri.
Da yake jawabi ga mambobin ƙungiyoyin biyu, Gwamna Lawal ya ce, shirin zai kai ga inganta hanyoyi a babban birnin jihar.
“Na ba da umarnin gina wuraren ajiye motocin tireloli a mashigun Gusau guda biyu: ɗaya a kan titin Funtua zuwa Gusau, ɗaya kuma a kan titin Sakkwato zuwa Gusau. Na gayyaci mambobin NARTO da PTD da su shiga cikin kwamitin don samar da wurin tsayawar ababen hawa.
“Za mu gudanar da cikakken buncike domin samun wuraren da suka fi dacewa da gina wurin ajiye tirelolin. Za mu yi la’akari da abubuwa da dama, kamar sauƙin zuwa wurin, buƙatuwa da kuma ƙarfin aljihun mu, ta yadda ba wai kawai don za su samar da kuɗaɗen shiga ga gwamnatin jihar ba ne, amma za su samar da yanayi mai kyau ga masu ziyarar jihar.
Shugaban ƙungiyar NARTO reshen Jihar Zamfara, Alhaji Mustapha Musa Sarkin Kagara, ya bai wa Gwamna Lawal tabbacin samun cikakken haɗin kan ’yan ƙungiyar kan wannan shiri.
Ya ce, “Za mu tabbatar da cewa ƙungiyar masu motocin haya ta Nijeriya NARTO da direbobin tankar mai (PTD) sun mara wa gwamnati wajen samar da wuraren tsayawar motocin."
"Muna cike da farin cikin wannan gayyata domin tattauna muhimman abubuwan da suka shafi aikin mu. Za mu bayar da cikakken haɗin kan mu wajen ganin an samar da wannan wuri na ya da zango ko ajiyar tirelolin. Wannan aiki zai samar wa kimanin mutum 5000 aikin yi a Zamfara. NARTO da PTD za su bayar da cikakken haɗin kai don samun nasarar wannan shiri."