An karrama tsohon gwamnan jihar Katsina da Digirin girmamawa a makarantar Kimiya da fasa ta Daura
- Katsina City News
- 24 Feb, 2024
- 504
Daga Shafin Mobile Media Crew
Cibiyar koyar da ilmin kimiyya da fasaha ta Gwamnatin tarayya dake Daura Jihar Katsina ta karrama tsohon Gwamnan Jihar katsina Rt.Hon. Aminu Bello Masari tare da ba shi digirin girmamawa.
A ranar asabar 24/02/2024, cibiyar ta karrama tsohon Gwamnan Rt. Hon. Aminu Bello Masari tare da digirin girmamawa, a matsayin shi na wanda ya bada gagarumar gudumuwa wajen kafuwar ita wannan Makarantar.
Cibiyar ta karrama tsohon Gwamnan yayin da ta ke bikin yaye Dalibanta 389, karo na farko, a harabar makarantar dake bisa hanyar zuwa Katsina cikin garin Daura.
Da yake gabatar da jawabin shi a wurin bikin, babban bako kuma daya daga cikin wadanda aka karrama Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Hon. Faruq Lawal Jobe.
Yace" Gwamnatin Jihar Katsina karkashin Rt. Hon.Aminu Bello Masari ta bada filin mazaunin makarantar na din-din-din da mazauninta na wucin gadi da ta ke zaune, a halin yanzu da kudaden fara tafiyar da makarantar a matakin farko.
Ya kara da cewa" Gwamnatin tsohon Gwamna Aminu Bello Masari ta bada mahimmanci ga bangaren ilmi fiye da kima, saboda sanin mahimmacin ilmi yasa Gwamnatin Malam. Dikko Umar Radda ta dora, ta ci gaba da bada fifiko ga bangaren ilmi.
Ya ci gaba da cewa" a cikin kokarin Gwamnatin Malam Dikko Radda, a bangaren ilmi, kwanan nan ta dauki 'yayan talakawa masu hazaka 40, ta tura su kasar Misira (Egypt) su koyo aikin kiwon lafiya.
Haka zalika ta bada tallafin kudi dubu dari biyar, biyar ga Dalibai masu koyon aikin lauya 'yan asalin Jihar Katsina. Daga karshe ya yaba ma makarantar akan wannan tunani da tayi na karrama mutanen da suka bada gudumuwa , a wajen kafuwar makarantar.
Shima da yake gabatar da jawabinsa amadadin sauran wadanda aka karrama tsohon Gwamna Aminu Bello Masari ya godema makarantar akan wannan karramawa da tayi ma shi tare da sauran mutanen da ta karrama, wanda su na cikin wadan da suka bada gudumuwar samuwar wannan makaranta.
Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya dauki lokaci yana bayani akan mahimmancin ilmi, inda yace" saka hannun jari a bangaren ilmi yana da matukar mahimmanci, domin saida ilmi ake samun ci gaba a rayuwa.
Bayan karrama tsohon Gwamnan da lambar yabo tare da ba shi digirin girmamawa, makarantar ta sanya sunan Rt. Hon. Aminu Bello Masari ga ginin ofisoshin harkokin mulki na makarantar watau (Rt. Hon. Aminu Bello Masari Administration Block).
Sauran wadan da aka karrama,akwai Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda, Sarkin Daura Mai martaba Alhaji Umar Faruq Umar, Kakakin Majalissar Dokoki na Kasa Hon. Tajuddeen Abbas, tsohon Sanatan shiyyar Daura marigayi Mustapha Bukar Madawakin Daura. Da dai sauran su.
Taron ya samu halartar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya samu wakilcin Alhaji Lawal Kazaure, Sanata mai wakiltar shiyyar Daura Sanata Nasiru Sani Zangon Daura, yan majalisu na tarayya, yan majalisu na Jiha, shugabannin kananan hukumomi. Da dai sauransu.