Kamfanin ATMOSFAIR Ya Gudanar Da Taron Wayar Da Kai Game Da Sabon Kirar Murhun Dafa Abinci
- Sulaiman Umar
- 21 Feb, 2024
- 464
Kamfanin "ATMOSFAIR SAVE80 CLEAN" Ya gudanar da taron wayar da kai kan sabon kirar murhun dafa abinci mai suna 'Save80 Clean Cooking Stove' a Katsina.
An gudanar da taron ne a Katsina Motel da misalin karfe 8 na safiyar yau Laraba yayin da dimbin jama'a musamman mata suka samu halarta.
A taron an koyar da yanda ake amfani da murhun tare da fadakarwa game da alfanunsa ga lafiyar al'ummah, tattalin arziki da kuma muhallli.