BANKWANA DA SHUGABANCIN MOPPAN – AHMAD SARARI
- Sulaiman Umar
- 01 Feb, 2024
- 568
Da suanan Allah mai rahama mai jinkai. Tsira da aminci su tabbata ga Manzon tsira Annabi Muhammadu S.A.W.
Ina mai godiya ga Allah S.W.T da ya nuna mana wannan rana kuma ya bamu ikon yin abinda ya samu na shugabancin kungiyar MOPPAN.
Duk abinda yake da farko yana da karshe, Allah ne kadai bashi da farko bashi da karshe. Kamar yau ne ‘ya’yan wannan masana’anta suka nemi na fito takarar zama shugaban kungiyar MOPPAN na kasa, na amsa kira akayi zabe kuma aka sami nasara sannan wa’adin farko ya kare aka sake neman na sake tsayawa duk da nayi furucin cewa bani da sha’awar cigaba. Cikin ikon Allah zangon farko na shekara 2 da zango na biyu na shekara 2 sunzo karshe.
Duk da dai taron koli (Congress) na kungiyar MOPPAN da akayi a ranar 10 ga watan Yuni 2023 ya amince da Karin shekara guda ga shugabanni na kasa da na jihohi bisa tsarin dake cikin sabon kudin tsarin mulki na MOPPAN (MOPPAN Constitution 2022). Sauka ta daga mukamina baiyi karo da kudirin taron kolin ba (National Congress), hakan yana da alaka ne da ra’ayina da akida ta. Sauran zababbu zasu ci gaba da shugabanci a karkashin jagorancin daya daga cikin mataimakana wanda yake kula da bangaren Arewa ta tsakiya wato Malam Habibu Muhammad Barde har izuwa 31/1/2025.
Mun dauki alkawarin yin duk wani aiki bisa doron kundin mulkin MOPPAN kuma munyi alkawarin rike amanar wannan kungiya da masana’anta. Mun gudanar da ayyukanmu bisa doron kundin tsarin mulkin kungiya. Sai dai dan kuskure na ajizanci da ba’a rasa ba.
Ina mai mika godiya ta ga dukkannin shugabannin MOPPAN da suka gabaceni da Amintattun MOPPAN da Abokan aikina da aka zabe mu tare da shugabannin jihohi. Godiya ta musamman ga masu sukar mu domin sune suka dinga farkar da mu in mun fara bacci.
Hakika mun sami nasarori masu dinbin yawa kuma mun gamu da kalubale kala kala sannan kuma mun gaza a wasu wuraren.
Zan bar MOPPAN mai cikakkiyar rijista, mai amintattun dattawa da Gwamnati ta sani, mai ofis da kayan ofis, mai “account” da isassun kudi a ciki. Zan bar kungiyar da ba bashi ko na kwabo akanta, kungiya mai rijista da kyakkyawar alaka da dukkannin hukumomin kasa da na jihohi.
Ina fata shugaban riko zai dora akan abin alkhairin da muka samar kuma zai gyara kurakuren da muka yi sannan ya cigaba da da ayyukan alkhairin da muka fara kuma ya gudanar da zabe bisa adalci. Da fatan ‘ya’yan wannan masana’anta zasu zakulo shugabanni na gari da zasu iya tunkarar sabon kalubalen da masana’antar take ciki.
Kafin ayi zaben MOPPAN a 2019, mun gabatar da kudirorinmu na irin aikin da zamu yi wato “Manifesto”. Munyi alakawarin:
1. DawodadarajarMOPPANmusammanaidonGwamnatidahukumomina kasa da jihohi.
2. Dawo da rijistar MOPPAN ta hukumar kula da kamfanoni ta kasa wato “CAC” da dawo da sunan kungiyar kan manhajar hukumar.
3. Gyarakundintsarinmulkinkungiya
4. Bawa kungiyoyin kwararru (professional guilds and Associations) damar
taka rawa a zaben MOPPAN na kasa
5. Farfadodaharkarkasuwancinfimamasana’antarKannywood
6. Horarda‘ya’yankungiyawajenkaramusuilimidadaburunyinfim
7. Sanar da ‘ya’yan masana’anta duk irin halin da kungiya ko masna’anta
take ciki.
Hakika mun sami cikakkiyar nasara akan kudirai na 1, 2, 3, 4, da na 5. An gudanar da kudurori na 6 da na 7 amma ba yadda aka so ba.
Akwai cikakkun bayanai na ayyukan da muka yi sama da 100 da irin nasarori da kalubale da gazawar da aka samu a lokacin wannan shugabanci, sannan akwai shawarwari.
A shirye nake na bawa sabon shugabanci gudunmawa da basu dukkannin bayanan da suke bukata.
A karshe ina mai neman gafarar duk wanda na batawa ko ina sane ko bana sane, nima na yafewa duk wanda ya bata min ko yana sane baya sane.
Allah ya taimakemu ya taimaki Kannywood ya sada mu da dukkannin alkhairan dake cikin wannan masana’anta ya kuma kare mu daga dukkannin sharrin dake cikinta.
Nagode
Ahmad Sarari