Barazanar Ƴan Ta'addar Daji Yasa Mutane Girbe Dawa Da Wake A Jihar Katsina
- Katsina City News
- 14 Nov, 2023
- 917
Manoma a ƙaramar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina sun fatsama gonakin su domin girbe amfanin gonakin su bisa barazanar ƴan ta'addar daji dake kora masu shanu suna cinye amfanin Gonar.
Da tsakar ranar yau dai ɓarayin suka kora shanun su gonar wani Alh. Umar Gaskora inda shi kuma ya ƙalubalance su akan mi zasu tura mashi shanu su cinye mashi amfanin gona, ƴan ta'addar basuyi wata wata ba suka halaka shi akan wannan yanzu haka yana Asibiti inda Likitoci suka tabbatar da Mutuwar shi.
Al'ummomin yankin Dankolo da Dugun Mu'azu dai suna cikin sun tashin hankali sun zama abin tausayi ganin cewa hatta da jami'an tsaro sojoji dake yankin sun kasa tabuka komai ganin cewa da inda ƴan ta'addar suke da kuma Inda ɓarayin suke cinyewa mutane amfanin gona baida wani nisa.
Waɗanda ɓarayin dai ba ƙaramar barazana bane a wannan yankin domin sun tarwatsa kasuwamcin yankin Sun tarwatsa kiwon yankin shima noman da kadai aka dogara dashi a yankin shima sun sako shi gaba, suna bin gonaki sua dibarwa mutane buhunnan amfanin gona yanzu Kuma sun koma suna cinyewa mutane dawa da farin wake.
Lamarin nan yafi ƙarfin jama'a su zuba Idanuwa ba tare da yin wani yunƙuri ba, muna kira gare su da su ci gaba da yin Addu'oen neman agajin gaugawa daga wurin Allah akan wannan Lamarin, Allah zai basu mahita kuma yayi masu maganin duk masu hannu akan wannan Ibtila'in.
Muhammadu Aminu Kabir