TARIHIN SARKIN KATSINA UMARUN DALLAJE
- Katsina City News
- 02 Nov, 2023
- 1543
Malam Ummaran Dallaje shi ne Sarkin Katsina na farko Bafulatani wanda ya fito daga wata zuriya mai suna Dallazawa.
Ya na daya daga cikin ‘yan gaba-dai gaba-dai
wajen gwabza yakin Jihadi a Birnin Katsinan Dikko har kuma suka samu nasarar kwace ikon tare da na danshi Malam Ummaru a matsayin Sarki.
An nuna an haifi Ummarun Dallaje a wani gari mai suna Dallaje a can gabashin garin Banye a kasar Hakimin Charanchi ta yanzu. Shi wannan suna Dallaje an samo shi ne daga wata kalma ta tsofon harshen Fulatanci watau Dallol
ko Dallal (Dal-lal) wadda ma’anarta ita ce Tsofon Dausayoi ko tsofuwar fadama ko kuma “je” ko “Ji” mahadin Magana ne na Harshen Fulatanci na dabarar nuna abubuwa ma su
yawa.
Ko kuma yadda Bahaushe ke amfani da ‘yar ko dan ko domin girka sunayen garuruwa watau kamar su ‘yarfadama ko Dangulbi ko Yartafki da dai sauransu. Watau dai ma’anarsa suna Dallaje ta yi kama da ‘yar Fadama.
Bincike ya nuna shi asalin Umarun Dallaje ba Bafulatani ba ne kamar yadda Bala Usman ya bayyana ya ce mahaifinsa Balarabe ne ko kuma ya fito daga cikin wasu mutane masu dangantaka da larabawa a can nahiyar nan ta Wadai ta kasar Chadi ta yanzu. Duk da ana da karfaffen zaton cewa mahaifiyarsa Bafulatana ce.
An ce Kakanninsa ne da jimawa suka yo kaura daga kasar Wadai suka zo Borno, daga nan suka kara tafowa yamma har suka zo kasar Katsina suka Zauna. Sunan mahaifinsa
Abdulmumini.
Ko da yake an ce asalinsa Balarabe ne, iyayen
kakanninsa sun fito ne daga wata kabila mazauniyar garin Ouaddai da ke kasar Chadi, sannu a hankali suka dawo daular Borno da zama, har kuma Kakanninsa suka taso
zuwa kasar Katsina inda suka soma zama a wani kauye mai suna Makar, daga nan suka koma Dasije, sannan sai suka dawo Dallaje da zama, anan ne kuma har akah aifeshi.
Malam Ummaru ya soma karafniyar daukar karatun Alkur’ani maigirma da na sauran littattafai tun yana yaro, yana zuwa
ga malamai don daukar darasi, har kuma ya hadu da Shehu Usman Danfodyo akan haka.
Daga bisani kuma bayan ya tumbatsa da ilimi, sai ya soma karantarwa da wa’azi a ciki da wajen kasarsu ta Katsina.
Don haka a wajajen shekarar 1803 miladiyya da Shehu Usman DanFodioyo ya ayyana yakin Jihadi da sarakunan Haɓe na kasar Hausa, Malam Ummaru na cikin wadanda suka mika wuya gami da amsa kiran Shehu Usmanu.
Don haka kasancewarsa malami Mai karantarwa, ya samu dalibai da suka sallama kansu gareshi don yin wannan yaki musamman daga garuruwan Dallaje, Rugar Bade, Sabon Gari da sauran wurare makwabta. Suka dunguma zuwa Gudu don hijira tare da Shehu Usmanu. An ce a wajajen karshen
shekarata 1805, bayan Muhammad Bello dan Shehu Usmanu ya aike Ummarun Dallaje don kai harin yaki izuwa garuruwan Alwasa da Alkalawa, daga nan kuma ya aike shi zuwa ga
wata rundunar masu jihadi da suka yada zango a gefen wani gari mai suna Ƴantumaki inda ya shaida mu su umarnin soma yaki a wannan yanki.
Ai kuwa babu ɓata lokaci suka soma kai hari gagaruruwa suna kwacesu. Kamar yadda maruwaitan tarihi suka ruwaito, an ce wannan runduna bata aukar daya kiga kowanne gari
haka kawai har sai sun yi kira gare su da haɓɓa ka sunnah, barin badi’o’I da shirka gami da tallafawa Shehu Usmanu a jihadinsa.
Da fari suna sanya mutum daya ne ya yi kiran
Sallah a gefen gari, domin sanar da mazauna garin zuwansu, daga nan sai su kira taron gaggawa da shugabannin garin, inda anan suke sanar musu da manufofinsu.
A cikins shekarata 1806, Malam Ummaru ya hadu da jagororin yakin Jihadi da suka fito daga Kano, Zazzau da sauran manyan kasashen Hausa a birnin Gada, inda aka
shirya wani gagarumin zaman tattaunawa karkashin Ikon Shugaban yakin Shehu Usmanu, sai dai an ba da uzurin cewa tsufa ya hana Shehu Usmanu yin wannan doguwar tafiya
daga mazauninsa na lokacin da ke Gwandu don halartar taron da a farko a ka tsara za’a yi shi a garin Magami, sai Muhammadu Bello ne ya wakilceshi dauke da sakonsa.
A yayin taron, Muhammad Bello ya nemi kowanne kwamandan yaki ya dauki rantsuwar yin biyayya ga umarninsa, gami da bin Sunnar Manzon Allah (S.A.W).
Wannan ke sanyawa wasu ke kallon asalin inda Muhammad Bello ya soma kafa kansa a matsayin Halifan Shehu Usmanu danfodiyo kenan.
A sakon da Shehu Usman Danfodiyo ya bayar zuwa wurin, ya karfafawa kwamandojinsa guiwarsa mun nasara da taimakon Allah ba da dadewa ba, sannan ya ja hankalinsu da kada su kasance ɓatattu masu aikata zalunci kamar
yadda Sarakunan da suke yaki da su suke, don haka yace musu su ji tsoron Allah, kuma su zamo masu hadin kai.
A wannan lokacin ne aka dankawa Ummarun Dallaje kwamandancin jihadin Katsina. Don haka bayan kammala taron ya kwashi tawaga zuwa Katsina. Abin da ya soma yi shi ne dates babbar hanyar shiga Katsina. Wadda kusan ta
wannan hanyar ne fatake ke shigar da kayayyakin abinci da na masurufi cikin birnin Katsina. Wannan abu shi ne ya sanya kunci ga mazauna birnin, har wasu suka rinka sulalewa ta sauran kofofin garin suna barinsa.
Da abin ya yi tsamari sai sarkin da kansa ya tashi da jama’arsa zuwa wani gari mai suna Dankama.
Hakan ya baiwa masu jihadi sukunin shigewa cikin birnin tare da karɓe ikonsa ba tare da gwabza yaki ba.
Daga bisani suka yi shirin yaki zuwa Dankama, suna gwabza yaki da Sarkin Katsina amma ba tare da sun samu nasara akan sa ba, ala tilas suka janye da baya suka komo katsina
da zama. Sai dai babu jimawa da hakan, Sai ga Sarkin Katsina ya iso da rundunarsa, inda ya auka musu da yaki kuma ya samu nasara a kansu. Ai kuwa ba shiri masu jihadi suka janye kamsu tare da komawa wani wuri mai suna
Sabon Gari da zama.
Shi kuwa Sarkin Katsina duk da wannan Nasara, bai kamu da shaukin cigaba da zamansa a birnin Katsina ba. Maimakon haka, sai ya dawo Dankama da zama, inda ya samu karin taimakon yaki daga Sarkin Kance. Ko da masu Jihadi suka sauka a Sabon Gari, sai suka dukufa nazarin yadda za su samu nasarar wannan yaki. Ai ku wannan haka sai ga shahararren jarumi Malam Muhammadu Namoda ya iso domin kawo musu dauki daga
Zamfara, babu jimawa kuma sai ga karin dakaru sun zo daga Daura da Kano. Daganan kuwa suka kara hada karfi da karfe,
suka fuskanci Sarkin Katsina inda suka kara gwabza gagarumin yaki a Dankama, a nan ne kuma har suka samu nasarar kashe Sarkin Katsina da kuma wasu manya daga
rundunarsa.
Wannan ya sa rundunar sarkin ta watse, wasu mabiyansa suka gudu izuwa Kwargon cikin kasar Damagaran, wasu kuma suka fantsama sauran sassa. Daga Kwargon dinsa mabiyan marigayi Sarkin Katsina Magajin Halidu suka karasa Damagaran, inda suka dora wani babba a cikinsu mai suna Dan kasawa wanda yake da ne ga tsaga-rana a matsayin shugabansu.
Su kuwa masu jihadi suka shiga birnin Katsina tare da zamo wa masu iko da shi karkashin shugabancin Kwamandan yaki Ummarun Dallaje.
Daga nan wadanda suka kawo gudunmuwa suka koma inda suka fito. Sai a karshen shekarata 1807, Amirul Muminina Shehu
Usmanu Danfodio, ya nada Ummarun Dallaje a matsayin Sarkin Katsina mai cikakken iko ta hanyar ba shi tuta. Sarki Ummaru ya cigaba da daura yaki ga sauran garuruwa makwabta, yana cinye duk garin da ya ki mika wuya a gare shi.
A kan haka ya gwabza yaki da sarkin Mani mai suna Mani Ibrahim Arne tare da halakashi. Sannan kuma ya kwace iko da garuruwan Maska da Goza ki a wuraren shekarata 1810
miladiyya. Daga cikin aikace-aikacen da ya yi shi ne na gina sabon masallacin jumu’a a birnin Katsina, sannan ya samar da sabbin tsare-tsaren gudanar da mulkin masarautar
katsina. Allah ya karɓi ran Malam Ummaru a cikin shekarar 1835 Miladiyya.
An ciro wannan tarihi ne daga cikin littafin Hazikin Marubuciin Sadik Tukur Gwarzo mai suna ‘Tarihin Jihadin Shehu Usmanu Danfodio A Kasar Hausa’.