"Asalin Sarautar Gwagware Tana Nufin Jarimta Da Sadaukarwa" -Mannir Shehu Wurma
- Katsina City News
- 01 Nov, 2023
- 724
Fassara: Zaharaddeen Ishaq Abubakar
Gwagwaren, Katsina – A ‘yan makonnin nan, hankalinmu ya karkata ga kokarin kawo sauyi da gwamnatin jihar Katsina ke yi, tare da mai da hankali musamman kan ayyukan tsaro. A yau, mun yi farin cikin haska labarin da ya zaburar da Gwamna Mallam Dikko Radda, wanda ya fito a matsayin ginshikin qarfi da jagoranci a cikin sarautar gargajiya ta Katsina.
Gwamna Radda, wanda shi ne shugaban jihar Katsina mai ci kuma mai kima da aka karrama da sarautar gargajiyar Katsina ta Gwagwaren Katsina A ma'anar Tarihi ko abinda Gwagware ke nufi shine Jarumta.
A tarihi anyi Jarumin (Gwagware) tun a karni na 17 wanda ya yi yaki da rashin adalci, tada kayar baya, da ‘yan fashi da makami a Katsina.
Gwagwaren karni na 20 Malam Dikko Umar Radda da salon shugabancin sa ya bambanta da saura, Gwamna Dikko Radda shi ne wanda jajircewarsa na ganin an samu zaman lafiya da tsaron al’ummar Katsina, al’amarin da ya bayyana tun kafin ya zama Gwamna. Ya samu sarautar Gwagwaren Katsina sama da shekaru goma sha biyar da suka gabata, wanda hakan ke nuna irin sadaukarwar da yake yi wajen kyautata rayuwar al’ummarsa.
'GWAGWARE' a sarautar Katsina na nuna jarumtaka, jajircewa, da sadaukarwa wajen fuskantar wahala. Gwamna Dikko Radda, bisa ga wannan abin da ya gada, ya dauki matakan da suka dace domin tunkarar kalubalen ‘yan fashi da makami da sauran matsalolin da suke kawo cikas, yana mai yakinin cewa, tare da ja-gorancin Ubangiji, za a iya shawo kan wadannan matsaloli.
Kaddamar da shirin tsaro na (Katsina Community Watch Corps) ya nuna wani sauyi. Wannan dai shi ne karon farko da al’ummar Katsina suka samu Gwamna mai zurfin fahimtar kalubalen da suke fuskanta kuma ya jajirce wajen ganin an magance wadannan matsaloli da gaske.
Bayyana wadannan matakan tsaro ya sa duk wani shedani ciki har da su kansu 'yan fashin cikin fargaba. Wadanda suka halarci taron kaddamar da zaratan masu kula da tsaron cikin al'umma na (Katsina community Watch Corps) ko suka ga faifan bidiyo a yanzu za su iya yin numfashi cikin sauki, suna da tabbacin cewa 'yan bindigar za su gamu da babbar matsala, don kuwa an kaddamar da wata rundunar aiki da hadin kai cikin al'umma
Kafin gabatar da ‘Gwagware’ don magance matsalar rashin tsaro, fata na ta dushewa, kuma da yawa sun yanke kauna saboda halin da suke ciki, ko kuma sun yi amfani da hanyoyin neman taimakon kai na wucin gadi.
Yunkurin da gwamnati ke yi na magance matsalar rashin tsaro yana misalta hanyoyin gudanar da ayyukan wannan cibiyar tsaro. Idan aka yi la’akari da girma da sarkakiyar lamarin, ya zama wajibi dukkanmu mu himmatu wajen tallafa wa wadannan yunƙurin ta hanyar samar da bayanai da kuma bayanan sirri ga jami’an tsaro, ta yadda za a tabbatar da samun gagarumar nasara.
Mannir Shehu Wurma wanda tsohon malami ne kuma shugaban karamar hukumar Kurfi a yanzu.